--
Kwararon robar wadanda suka kwanta damu muke kaiwa bokaye - Karuwai

Kwararon robar wadanda suka kwanta damu muke kaiwa bokaye - Karuwai

- Jami’an ‘yan sanda a Najeriya sun kama wasu dalibai mata hudu na jami’a dauke da kwaroron roba da ke kunshe da maniyyi a ciki - Daliban hudu duk ‘yan makaranta ne ta gaba da sakandare a jihar Akwa Ibom kuma an kama su ne sakamakon bayanan sirri da ‘yan sandan suka samu

 - Ta ce hausawan da ke siya suna kaiwa Alhazawan Abuja da Legas ne wadanda suke yin duk tsafin da suke bukata da shi Jami’an ‘yan sanda a Najeriya sun kama wasu dalibai mata hudu na jami’a dauke da kwaroron roba da ke kunshe da maniyyi a ciki. Daliban hudu duk ‘yan makaranta ne ta gaba da sakandare a jihar Akwa Ibom kuma an kama su ne sakamakon bayanan sirri da ‘yan sandan suka samu dangane da daliban. 

Daliban masu karantar fannin karatun jarida a makaranta, sun bayyana cewa suna karuwanci don suna kwanciya da maza kala-kala. Bayan kwanciya kuwa da mazan, suna daukar kwararon robar da suka yi amfani da shi don siyarwa da hausawa a jihar da tsada. 


 Kwararon robar wadanda suka kwanta damu muke kaiwa bokaye - Karuwai Source: Facebook

Kamar yadda ‘yan matan suka sanar, sun fada wannan kasuwancin ne tun kusan shekaru uku da suka gabata bayan sun fara karatu. Glory Edet, daya daga cikin ‘yan matan ta ce a kowanne lokaci ta kwanta da namiji, da kanta take cire kwararon robar da nufin ta damu da namijin. Daga nan sai tayi tamkar za ta yadda shi amma sai ta kulle shi a leda ta jefa a jakarta. 

Ta ce hausawan da ke siya suna kaiwa Alhazawan Abuja da Legas ne wadanda suke yin duk tsafin da suke bukata da shi. Kamar yadda suka ce, sa’arsu ta zo karshe ne bayan da makwabciyarsu ta ji da yadda suke rayuwa sannan ta kaiwa ‘yan sanda rahoto. 


LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y

KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




0 Response to "Kwararon robar wadanda suka kwanta damu muke kaiwa bokaye - Karuwai "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?