--
NCC ta bayyana dalilin sake rufe wasu layukan waya miliyan 2.2

NCC ta bayyana dalilin sake rufe wasu layukan waya miliyan 2.2

Hukumar kula da harkokin kamfanonin sadarwa na kasa (NCC) ta sanar da cewa ta sake rufe wasu layukan waya (SIM) saboda rashin yi musu rijista ta hanyar da ya dace. A cikin wata sanarwa da shugaban hukumar NCC, Farfesa Umar Dambatta, ya fitar ranar Lahadi, 

Ya bayyana cewa yanzu an rufe wani layin waya na kamfanonin sadarwar da ke Najeriya, ya ce an rufe layukan ne saboda rashin yi musu rijista bisa ka'ida. A kwanakin baya ne ministan harkokin sadarwa, Dakta Isa Pantami, ya umarci hukumar NCC ta rufe dukkan wasu layukan wayar hannu da basu da rijista ko kuma ba a yi musu rijista ta hanyar da ya kamata ba. 

Bayan wannan umarni, rahotanni sun rawaito cewa Dakta Pantami ya sake bayyana cewa bai kamata mutum daya ya mallaki layukan waya fiye da uku ba, a saboda haka NCC za ta dauki mataki a kan 'yan Najeriya masu layukan waya fiye da uku. 


LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y

KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




0 Response to "NCC ta bayyana dalilin sake rufe wasu layukan waya miliyan 2.2 "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?