MUJALLAR LABARAI, ROHOTANNI, BINCIKE, SHARHI, AL'AJABI, ILMANTARWA FADAKARWA DA NISHADANTARWA "Colour"
 • Latest News

  Latsa Koren Hoton Dake Qasa Domin Sauke Manhajar Labari Awayarka Ta Hannu Kyauta

  Sunday, March 8, 2020

  Jami'an FRSC sun fasa tayar motar matar da ta dauko mai nakuda (Bidiyo)
  - Wani mutum dan asalin garin Fatakwal ya wallafa wani bidiyon jami’an FRSC suna fasa tayar motar ‘yar uwarshi yayin da take kai mai nakuda asibiti - FRSC din sun zargi matar da kin saka damarar da ke kan kujerar sannan suka ci ta tarar N20,000 - Rashin kudin biyan ne yasa suka sace tayar motar duk da bayanin da tayi musu na cewa kidima ce ta hana ta saka wa Wani mutum mai suna Port Harcout Cabman, 


  a shafinsa na twitter ya zargi wasu jami’an kiyaye hadurran kan titi da mugunta. Mutumin ya wallafa bidiyo ne inda ya zargi jami’an da fasa wa wata mata tayar mota wacce yace ‘yar uwar shi ce. Ta bayyana cewa tana hanzarin kai mace mai nakuda asbiti ne saboda kidimewa ta manta bata saka damarar da ke kujerar tukin ba.


  Kamar yadda wanda ya wallafa bidiyon ya sanar, laifin ‘yar uwar shi din shine rashin biyan naira dubu ashirin din da suka bukaceta da ta biya. Ya yi ikirarin cewa ‘yar uwar shi din ba gudu take da motar ba ko kuma tukin ganganci. Hakazalika sun tuhumi matar mai nakudar da rashin saka damarar amma sai ta sanar dasu cewa ba za ta iya jure damarar ba. Saboda tana cikin tsananin ciwon nakuda ne. A matsayin ladabtarwa kuwa, sai jami’an suka bukaci kudi har naira dubu ashirin amma da suka kasa bayarwa sai suka fasa musu tayar motarsu.
  LATSA NANπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y

  KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  KAYI TAMBAYA ANAN KOKA FADI RA'AYINKA AKAN ABINDA MUKEYI

  Item Reviewed: Jami'an FRSC sun fasa tayar motar matar da ta dauko mai nakuda (Bidiyo) Rating: 5 Reviewed By: Admin
  AIKA LABARI