--
Rusau: El-Rufa'i ya bawa 'yan 'kasuwar bacci' wa'adin kwana uku

Rusau: El-Rufa'i ya bawa 'yan 'kasuwar bacci' wa'adin kwana uku



Gwamnatin jihar Kaduna ta ba wa ‘yan Kasuwar Barci da ke Tudun Wada a Kaduna wa’adin kwanaki uku. An manna sanarwan ne a shagunan da ke kasuwar a safiyar Asabar kuma an umarci ‘yan kasuwar dasu bar kasuwar zuwa ranar Litinin. 


Shugaban kungiyar ‘yan kasuwar, Haruna Dabai, ya sanar da jaridar Daily Trust cewa hankulan ‘yan kasuwar ya matukar tashi. “Mun zo kasuwar da safiyar Asabar inda muka samu sanarwar an manna a shagunanmu. An bamu kwanaki uku a kan mu tashi. Mun yi magana da lauyanmu amma kamar yadda kuke gani, lamarin ya faru ne a ranakun karshen mako.

Rusau: El-Rufa'i ya bawa 'yan 'kasuwar bacci' wa'adin kwana uku Source: UGC 


Muna kira ga ‘yan kasuwar da su kwantar da hankulansu don muna kokarin ganin yadda zamu shawo kan matsalar cikin lumana,” yace. Jaridar Daily Trust ta ga takardar wacce daraktan KASUPDA, Isma’il Umar-Dikko yasa hannu da kwanan wata 6 ga watan Maris. Babban daraktan ya ce hakan ya zama dole,


idan aka yi duba da yadda gwamnatin jihar Kaduna ta dage wajen aiyukan gyaran kasuwannin jihar. “Rashin biyayya ga wannan umarnin zai jawo hukumar ta rushe shagon duk yadda ta same shi, kamar yadda sashi na 60 na dokokin KASUPDA na 2018 ya tanadar.” Takardar ta ce. LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y

KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




0 Response to "Rusau: El-Rufa'i ya bawa 'yan 'kasuwar bacci' wa'adin kwana uku "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?