\ Najeriya: An Bada Umurnin Yin Amfani Da Miliyan 620 Don Dakile Cutar Coronavirus - BZGLOBALSERVICE.COM.NG Najeriya: An Bada Umurnin Yin Amfani Da Miliyan 620 Don Dakile Cutar Coronavirus - BZGLOBALSERVICE.COM.NG
 • LABARAN YAU

  Saturday, March 7, 2020

  Najeriya: An Bada Umurnin Yin Amfani Da Miliyan 620 Don Dakile Cutar Coronavirus


  A daidai lokacin da Majalisar dokokin Najeriya ta bayyana fargabanta akan shigowar cutar Coronavirus har ma ta yi tunanin dage zamanta,

  Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan ya jagoranci wata tawaga da ta kunshi wasu abokanan aikinsa kai ziyarar ganin irin matakan da gwamnati ke dauka na samun wurin killace duk wani da aka samu da cutar Coronavirus.

  Tawagar ta yi tattaki ne zuwa babban asibitin gwamnati dake Gwagwalada a Abuja, babban birnin tarayyar kasar inda ake aikin gina wuraren killacewar.

  Shugaban majalisar ya nuna bacin ransa ganin yadda aikin ke tafiyar hawainiya. Ya kuma ba Ministar Kudi, Zainab Shamsunah Ahmed umurnin ta yi gaggawar sakin kudi kimanin Naira Miliyan 620 ga Cibiyar Kula Da Cututtuka ta kasar, saboda a gaggauta kammala aikin, duk da cewa har yanzu ba a samu wani wanda ya kamu da cutar ba, bayan dan asalin kasar Italiyar nan da ya shigo Najeriya da cutar, wanda aka killace a wani asibiti dake jihar Legas.
  Hassan Mohammed Nasiha Jarman Gusau, yana daya daga cikin Sanatocin da suka kai ziyarar ya ce, duk da cewa gwamnati ba ta yi gaggawar aikin dakile yaduwar cutar ba, yana ganin za a gama aikin cikin lokaci domin a matsayin su na masu yin doka kuma shugabanni, za su sa ido su ga cewa komai ya tafi daidai.

  A bangaren Majalisar wakilai kuma, mahawara ce ta kaure akan cutar Coronavirus inda a karshe majalisar ta yi amai ta kuma lashe akan batun zuwan su hutu saboda bullar cutar, har ma ta ce ta janye batun zuwa hutun saboda korafe korafen al’umma, a cewar dan Majalisa Sada Soli Jibiya.

  Dan majalisar ya kara da cewa wasu kasashe irin su China, Japan, Hong Kong da Iran sun rufe Majalisun su, amma su ba za su tafi hutu ba saboda kar a kawo rudani a cikin kasa.


  LATSA NANπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y

  KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  KAYI TAMBAYA ANAN KOKA FADI RA'AYINKA AKAN ABINDA MUKEYI

  Item Reviewed: Najeriya: An Bada Umurnin Yin Amfani Da Miliyan 620 Don Dakile Cutar Coronavirus Rating: 5 Reviewed By: Admin
  site-verification: 8b0db1c078bc0934ee385b3afb5129be