--
Gwamnatin Tarayya ta fadi dalilin jinkirin biyan 'yan N-Power Albashi

Gwamnatin Tarayya ta fadi dalilin jinkirin biyan 'yan N-Power Albashi




Ministar walwala da jin kan 'yan kasa, Hajiya Sadiya Farouq ta yi bayanin dalilin da yasa gwamnatin tarayya ba ta biya ma'aikatan N-Power ba. 


Ministan ta ce wannan tsaikon ya faru ne saboda ma'aikatar na son ganowa da tantance duk masu morar shirin da aka dinga biya kafin ta karba ma'aikatar. Ma'aikatar ta bayyana cewa, ta bukaci wadanda ke rike da ma'aikatar kafin zuwanta da su bada bayanin kudade da kuma wadanda aka biya kafin zuwan ministar. 





Shi dai shirin N-Power an yi shi ne don horarwa tare da samar da aikin yi ga matasa marasa abin yi a Najeriya masu shekaru tsakanin 18 zuwa 35 a fadin kananan hukumomi 774 na kasar nan. A ranar 25 ga watan Fabrairun 2020, ministar ta bayyana cewa mutane 473,137 ne ke morar shirin.


 Ministar ta sanar da hakan ne a ranar Litinin a garin Abuja yayin da ta ziyarci kwamitin yaki da talauci na majalisar wakilai. Kwamitin ya samu shugabancin ya samu shugabancin Hon. Abdullahi Salame. 


Gwamnatin Tarayya ta fadi dalilin jinkirin biyan 'yan N-Power Source: UGC 


A tsaikon da aka samu kan biyan masu morar shirin: "Na san mun samu korafi a watan Oktoba yayin da muka shigar da shirin NSIP a ma'aikatar kuma muke bukatar fahimtarsa. Ya kamata mu gane komai kafin mu fara sa hannu a kan fitar da manyan kudade kuma hakan ne yasa muke samun tsaiko. 



Bayan mun fara aikin tare da wani babban sakatare a watan Janairu, sai muka samu canji wanda kuma shi ma yana bukatar fahimtar komai." A yayin karin haske a kan tsaikon biyan kudin da aka samu, Tijjani Umar babban sakataren ma'aikatar ya ce: "A lokacin da na dawo ma'aikatar, na gano cewa gwamnati na kashe makuden kudi a kan shirin.




Kudin na da yawa, don haka muke bukatar karantawa tare da fahimtar komai. Dole ne mu yi hakan ta yadda zamu iya kare abinda muke fitarwa." Ya kara da cewa "mun fitar da bayani a kan cewa za a samu tsaiko wajen biyan kuma hakan zai biyo bayan kokarin fahimtar lamarin saboda kudaden na fita a biliyoyin nairori ne. Ba zai yuwu mu ci gaba da gini a kan abinda bamu sani ba." 




LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y

KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




0 Response to "Gwamnatin Tarayya ta fadi dalilin jinkirin biyan 'yan N-Power Albashi"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?