--
Majalisar dattijai za ta haramta shigo da janareto, shekaru 10 ga masu laifin

Majalisar dattijai za ta haramta shigo da janareto, shekaru 10 ga masu laifin


- Majalisar dattijan kasar nan ta fara yunkurin saka dokar daure duk wanda ke siya da siyar da injin samar da wutar lantarki na shekaru 10

- Dokar haramta amfani da janareto an karanta ta karo na farko ne a zaman majalisa a ranar Laraba

- Mataimakin shugaban kwamitin noma da raya karkara, Sanata Muhammed Enagi Bima na jam’iyyar APC ne ya dau nauyin dokar
Majalisar dattijan kasar nan ta fara yunkurin saka dokar daure duk wanda ke siya da siyar da injin samar da wutar lantarki na shekaru 10. Dokar na son hana shigowa da kuma amfani da janareto a kasar nan tare da shawo kan gurbacewar iska.

Dokar haramta amfani da janareton an karanta ta karo na farko ne a zaman majalisa a ranar Laraba. Mataimakin shugaban kwamitin noma da raya karkara, Sanata Muhammed Enagi Bima na jam’iyyar APC ne ya dau nauyin dokar.

Da wannan dokar da ake son tabbatarwa, ana bukatar kowa ya daina shigowa da kayyayakin samar da wutar lantarki masu amfani da fetur ko kalanzir a duk fadin kasar nan.

Duk kuwa wanda aka kama da wannan laifin za a gurfanar dashi a gaban kotu tare da yanke mishi hukuncin a kalla shekaru 10 a gidan gyaran hali.

Amma kuma yadda sanatan da ya kai bukatar gaban majalisar ya bayyana, wannan haramcin ba zai hada da amfanin asibitoci ba, filayen sauka da tashin jiragen sama, filayen jjiragen kasa, cibiyoyin bincike da sauransu wadanda suke bukatar wuta na sa’o’i 24 a kowacce rana.


LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y


KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




0 Response to "Majalisar dattijai za ta haramta shigo da janareto, shekaru 10 ga masu laifin"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?