MUJALLAR LABARAI, ROHOTANNI, BINCIKE, SHARHI, AL'AJABI, ILMANTARWA FADAKARWA DA NISHADANTARWA "Colour"
 • Latest News

  Latsa Koren Hoton Dake Qasa Domin Sauke Manhajar Labari Awayarka Ta Hannu Kyauta

  Saturday, March 14, 2020

  An tabbatar da samun cutar Coronavirus a jikin shugaban kasar Brazil Jair Bolsonaro


  - Wani gwaji da aka gabatar akan shugaban kasar Brazil Jair Bolsonaro ya tabbatar da cewa yana dauke da cutar Corona mai kisa

  - An gabatar da gwajin ne bayan an samu cutar a jikin daya daga cikin mataimakansa a gwamnati 

  - Hakan ya zo ne kwanaki kadan bayan ya gana da shugaban kasar Amurka Donald Trump An tabbatar da shigar cutar Corona jikin shugaban kasar Brazil Jair Bolsonaro. Dan gidan Bolsonaro, 

  Eduardo shine ya sanar da Fox News yace yanzu haka suna cigaba da gabatar da gwaji a jikin shi domin nemo hanyar da za a bullowa lamarin. Eduardo ya kara da cewa suna tsammanin fitar sakamako na biyu akan gwajin zai fito nan bada dadewa ba. 

  An samu sakamakon cutar a jikin nashi ne kwanaki kadan bayan Bolsonaro ya gana da shugaban kasar Amurka Donald Trump a Mar-a-Lago. Bayan fitar wannan labari a kasar ta Brazil, an kira duka masu fada a ji na kasar, inda suka gabatar da taron gaggawa a ofishin shugaban ma'aikata, kamar yadda Fox News ta ruwaito. An gabatar da gwajin a jikin Bolsonaro ne bayan daya daga cikin mataimakansa, wanda shima ya halarci wani taro a birnin Florida aka same shi da cutar ta COVID-19.

  Haka shima sakataren sadarwa na shugaban kasar Fabio Wajngarten, mai shekaru 64 a duniya wanda shi ma ya kai ziyara birnin Miami, an ga alamun cutar a jikinshi, inda aka gabatar da gwaji kuma aka tabbatar da ita a jikinshi. Wannan dai na zuwa ne bayan Peter Dutton, ministan cikin gida na kasar Australia ya kamu da cutar, bayan ya dawo daga birnin Washington D.C, inda ya gana da Attorney General William Barr da kuma Ivanka Trump.LATSA NANπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y


  KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  KAYI TAMBAYA ANAN KOKA FADI RA'AYINKA AKAN ABINDA MUKEYI

  Item Reviewed: An tabbatar da samun cutar Coronavirus a jikin shugaban kasar Brazil Jair Bolsonaro Rating: 5 Reviewed By: Admin
  AIKA LABARI