--
Mace mai kamar Maza: Tsohuwa yar shekara 70 ta yi sanadiyyar mutuwar yan bindiga 40

Mace mai kamar Maza: Tsohuwa yar shekara 70 ta yi sanadiyyar mutuwar yan bindiga 40

Masu iya magana kan ce “Mace mai kamar maza kwari ne babu” wannan magana na masu hikima ya tabbata a kan wata mata dattijuwa mai shekaru 70 a duniya, wanda aka sakaya sunanta, da ta jagoranci matasa mafarauta zuwa cikin dazuka inda suka kashe yan bindiga 40 a jahar Neja. 

Jaridar Blueprint ta ruwaito guda daga cikin mafarautan dake cikin tawagar wannan jaruma, Mallam Alhassan ya bayyana cewa ta jagorance su zuwa cikin dajin Zuguruma a karamar hukumar Mashegu na jahar, inda a can suka yi artabu da yan bindiga. 

A cewar Alhassan, shigarsu dajin ke da wuya sai suka fara harbe harbe a sama da nufin janyo yan bindigan daga mabuyarsu a wani sabon salon dabarar yaki. “Suna fitowa sai suka dinga harbin mai kan uwa da wabi ba tare da wani takamaimen inda suke harbi ba. 

“A haka har harsashinsu ya kare, daga nan muka dira a kansu har sai da muka kashe guda 40, mun kwato bindigu samfuri daban daban da sauran makamai wanda muka mika hukumar Yansanda.” Inji shi. Sai dai da majiyarmu  ta tuntubi hukumar Yansandan jahar domin tabbatar da labarin, sai ta ce ba zata ce komai ba a yanzu sakamakon har yanzu ana cigaba da kaddamar da hare haren. 

A nata bangaren, gwamnatin jahar Neja ta jinjina ma namijin kokarin da mafarautan suke yi tun bayan da gwamnan jahar, Abubakar Sani Bello ya amince da sanyasu cikin harkar tabbatar da tsaro tare da yaki da yan bindiga. Mai magana da yawun gwamnan, Mary Noel Barje ce ta tabbatar da haka inda ta ce gwamnan ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi a taron al’ummar Zuru, inda ya jinjina ma kokarin mafarautan, 

ya ce hakan ya zama wajibi duba da rikicin da yan bindiga suke haifarwa a jahar. LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y

KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE FINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 


0 Response to "Mace mai kamar Maza: Tsohuwa yar shekara 70 ta yi sanadiyyar mutuwar yan bindiga 40 "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?