MUJALLAR LABARAI, ROHOTANNI, BINCIKE, SHARHI, AL'AJABI, ILMANTARWA FADAKARWA DA NISHADANTARWA "Colour"

Kusauke Manhajar Bzglobalservice.com.ng Acikin Wayoyinku Na Android Kyauta Domin Samun Labarai

MUNA SIYAR DA DATA TA SHIGA YANAR GIZO TA KAMFANIN MTN DOMIN SIYA DANNA HOTON DAKE QASA YANZU

 • Latest News

  Tuesday, March 24, 2020

  Labari da duminsa: Ma'aikatan Aso Villa 3 sun kamu da cutar Coronavirus

  Rahoto daga TheNation na nuna cewa ma'aikatan ofishin shugaban ma'aikatan fadar shugaban, Abba Kyari, guda uku sun kamu da cutar Coronavirus (COVID-19). An yi yunkurin ji daga bakin masu magana da yawun shugaban kasa amma ba a samu nasara ba saboda gaba daya ba a ga Garba Shehu da Femi Adesina a fadar ba.

  Majiya daga fadar shugaban kasan wanda ya bukaci a sakaye sunansa ya tabbatar da cewa an shawarci dukkan mutanen da suka yi hulda da Abba Kyari. Ya ce ana kyautata zaton cewa hakan yasa ma'aikatan fadar shugaban kasa basu zo aiki yau ba. Bugu da kari, dukkan ma'aikatan mataimakin shugaban kasa, Yemo Osinbajo, basu shiga fadar ba a yau illa mai magana da yawunsa. A yanzu dai, da alamun ana shirin kulle fadar shugaban kasar saboda an umurci dukkan dukkan ma'aikatan su koma gida.

  Labarin mai inganci daga wakilinmu dake jihar Bauchi na nuna cewa gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed Kauran Bauchi, ya kamu da cutar Coronavirus. A wani jawabin da mai magana da yawun gwamnan, Muhktar M Gidado ya saki, ya tabbatar da rahoton inda ya bukaci alumma su taimakawa gwamnan da addu'o'i.

  Jawabin yace “Muna sanar da daukacin jama“a cewa sakamakon gwajin mutane shida da cibiyar takaita yaduwar cututtuka ta gudanar kan gwamna Bala AbdulKadir Mohammed, iyalansa, da hadimansa da suka raka sa Legas ya fito.“ “Daga cikin sakamakon shida na mutum daya kadai ya tabbata ya kamu, kuma shine na Sanata Bala AbdulKadir Mohammed, gwamnan jihar Bauchi.“
  LATSA NANπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP  https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y


  KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  KAYI TAMBAYA ANAN KOKA FADI RA'AYINKA AKAN ABINDA MUKEYI

  Item Reviewed: Labari da duminsa: Ma'aikatan Aso Villa 3 sun kamu da cutar Coronavirus Rating: 5 Reviewed By: Admin
  AIKA LABARI