--
Jerin manyan mutanen da su ke dauke da kwayar cutar COVID-19 a Yau

Jerin manyan mutanen da su ke dauke da kwayar cutar COVID-19 a Yau

Akalla mutane 97 ne ake da labarin su na dauke da cutar COVID-19 a Ranar 28 ga Watan Maris 2020, kamar yadda hukumar NCDC mai takaita yaduwar cututtuka ta bayyana. Kawo yanzu an yi wa mutane fiye da 150 gwaji a Najeriya,

inda aka tabbatar da cewa an samu mutane 97 da su ka kamu da wannan cuta ta COVID-19 mai hana numfashi. Daga cikin shaharrun wadanda aka tabbatar sun kamu da wannan cuta akwai: 1. Abba Kyari Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari, ya kamu da wannan cuta bayan wasu tafiye-tafiye da ya yi zuwa Jamus da wasu kasashe. Ana tunanin cewa Kyari ya na jinya a asibiti.



 2. Bala Abdulkadir Mohammed Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya na cikin wadanda wannan cuta ta yi wa kamu a Najeriya. Gwamnan ya hadu da Mohammed Atiku, kuma ya fita ziyara kasar waje kwanaki.




 3. Nasir El-Rufai A Ranar 28 ga Watan Maris, gwamnnan Kaduna Nasir El-Rufai ya tabbatarwa mutanen jiharsa cewa ya kamu da Coronavirus. Hakan na zuwa ne bayan gwamnan ya dauki matakin kare jihar.



4. Mohammed Atiku Abubakar Alhaji Mohammed Atiku Abubakar ya na dauke da cutar COVID-19. Mahaifinsa, Atiku Abubakar, ya tabbatar da cewa ‘Dansa ya kamu, amma ana kula da shi a asibitin Gwagwalada da ke Abuja. 




 5. Abokan Bala Mohammed Daga cikin na-kusa da gwamnan Bauchi, akwai wani Amininsa mai shekaru 62 da ya kamu da wannan cuta. Gwamnatin jihar Bauchi ba ta bayyanawa kowa sunan wannan Bawan Allah ba. 6. Chioma Rowland Shararren Mawaki Davido, ya bayyana cewa Mahaifiyar ‘Dansa kuma wanda zai aura, Chioma Rowland ta kamu da cutar COVID-19. Chioma ta bayyana wannan da kanta a shafin Tuwita.



7. Suleiman Achimugu Injiniya Suleiman Achimugu ya na cikin wadanda su ka fara kamuwa da COVID-19 bayan zuwansa Ingila. Tun a makon jiya cutar ta kashe tsohon shugaban hukumar PPMC na kasa.
LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP  https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




b

0 Response to "Jerin manyan mutanen da su ke dauke da kwayar cutar COVID-19 a Yau "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?