--
Coronavirus: Fadar shugaban kasa ta yi magana a kan ba wa kowanne dan kasa N30,000

Coronavirus: Fadar shugaban kasa ta yi magana a kan ba wa kowanne dan kasa N30,000

- Fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta karyata rahoton da ke bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta ba wa 'yan kasa N30,000

- Kamar yadda Femi Adesina ya bayyana, rahoton an danganta shi da shi ne amma bashi da tushe balle makama - A cewar rahoton bogin, gwamnatin tarayya ta ware biliyoyin naira don tallafawa miliyoyin 'yan Najeriya saboda muguwar cutar coronavirus Fadar shugaban kasa ta karyata rahoton da ke ta yawo a yanar gizo mai bayyana cewa gwamnatin tarayya na shirin ba wa duk dan Najeriya da ke da BVN N30,000. An danganta rahoton da mai bada shawara na musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan yada labarai, Femi Adesina.

Tuni kuwa Adesina ya karyata labarin sannan ya ce mara tushe ne balle makama, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito. Kamar yadda Adesina ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce: "Masu shirya labaran bogi a yanar gizo sun bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta kowanne dan Najeriya mai BVN N30,000 don taimaka musu wajen siyen abubuwan bukata kafin a rufe hanyoyin shige da fice a kasar.

Wannan ba daga ni yake ba, ba ni na sanar ba." Kamar yadda rahoton bogin ya bayyana, gwamnatin tarayya ta ware biliyoyin nairori don taimakawa 'yan Najeriya miliyan 40 da N30,000 kowanne. Wannan tallafin a cewar rahoton bogin, hakan zai taimakawa 'yan Najeriya masu karamin karfi sakamakon illar da muguwar cutar Coronavirus tayi wa kasar.


LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP  https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




b

0 Response to "Coronavirus: Fadar shugaban kasa ta yi magana a kan ba wa kowanne dan kasa N30,000"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?