LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Dalilin da yasa muka yi sallar Juma'a duk da dokar gwamnati - Sheikh JingirShugaban kungiyar Jamma'atu Izalatil Bisa Waikamatis Sunnah (JIBWIS), Sheikh Sani Yahaya Jingir ya ce shi sauran yan kungiyar sun yi sallar Juma'a ne a jihar domin Gwamna Simon Lalong bai hana su yin sallar ba. A cewar Sheikh Jingir tunda ba a samu bullar cutar ba a jihar babu dalilin da zai sa a hana yin sallar ta Juma'a. Dubban mutane sun halarci sallar da Juma'a da aka gudanar a Jos babban birnin jihar ta Plateau.

Daily Trust ta ruwaito cewa anyi sallar Juma'ar a dukkan masallatai da ke karkashin kungiyar ta JIBWIS. Ma'ajiyar Legit.ng ta ruwaito cewa kungiyar Jamma'atu Nasril Islam (JNI) ta bayar da umurnin kada a fito sallar a babban masallacin Plateau da sauran masallatai da ke karkashin ta.

Daily Trust ta ruwaito yadda jami'an yan sandan Operation Safe Haven (OPSH) da aka aike garin na Jos a yammacin ranar Alhamis suka rika bi cikin gari suna shella cewa ba za a yi sallar Juma'ar ba a masallatai. Jami'an tsaron sun riƙa amfani da na'urar amsa kuwwa suna shaidawa al'umma cewa ba za ayi sallar Juma'a ba kuma ba za a tafi coci ba a ranar Lahadi. Anyi sallar na jiya Juma'a ne kwana guda bayan gwamnatin jihar ta bayar da umurnin a kama duk wanda ya karya dokar da aka kafa a jihar domin kiyaye yaɗuwar annobar Coronavirus.

Kwamishinan labarai na jihar, Mista Dan Magaji a ranar Juma'a cikin wata sanarwa ya ce Gwamna Lalong ya ce "ana gargadin mutanen jihar su yi biyayya ga dokar ta zama a gida domin an bawa jami'an tsaro umurnin hukunta duk wanda aka samu ya karya dokar. Kafin a fara sallar Juma'ar ta jiya, jami'an tsaro da dama da suka hada da sojoji, Civil defence, Yan sanda sun taru a kusa da masallacin Yantaya domin tabbatar da dokar amma kwatsam suka bar wurin domin bawa mutanen da suka fito yin sallar damar hakan. Wata ƙwakwarar majiya daga rundunar soji ta shaidawa Daily Trust cewa akwai yiwuwar an umurci jami'an tsaron su bar wurin ne domin gudun afkuwar fitina.
LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP  https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1YKU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 
b

Post a comment

0 Comments