--
Jennifer Haller: Mace ta farko a duniya da aka fara gwada maganin Coronavirus a jikinta

Jennifer Haller: Mace ta farko a duniya da aka fara gwada maganin Coronavirus a jikinta

Wata mata mai shekaru 43 a duniya ta zama mutum ta farko a duniya da aka yiwa allurar gwajin maganin cutar Coronavirus Bayan fara gabatar da gwajin, Jennifer Haller ta zama ta farko da aka fara gabatar da gwajin a jikinta. Gwajin wanda aka fara shi kwanan nan, 

Dr Lisa Jackson ta jagoranci gwajin, wacce take babbar ma'aikaciya a cibiyar lafiya ta Seattle dake birnin Washington, birnin da yafi ko ina yawan mutanen da suka kamu da cutar a kasar Amurka, inda mutane 42 suka mutu a cikin mutane 69 na kasar.

Jennifer Haller ta yi magana akan wannan gwaji da aka gabatar a kanta, inda ta ce: "Hankalin mu duka a tashe yake saboda wannan cutar, saboda haka nake ganin kamar wannan wata dame ce a wajena a fara gabatar da gwajin a kaina." 

 An zabi mutane wadanda za a gabatar da gwajin a kansu da suke tsakanin shekaru 18 zuwa 55, inda ba wai iya lafiyar maganin za a duba ta maganin ba, ana so a gano yadda mutum zai yi bayan gabatar da gwajin a jikinshi. Nan da makonni shida,

 za a sake gabatar da gwajin akan mutane 45. Wannan dai na zuwa ne bayan cutar ta Coronavirus wacce ta samo asali a kasar China ta girgiza ko ina na kasashen duniya. Cutar wacce a yanzu ta shiga kusan dukanin kasashen duniya an kasa gano ainahin maganinta. Sai dai a wannan karon kasar ta Amurka ta gabatar da gwajin a karon farko. LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y


KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




0 Response to "Jennifer Haller: Mace ta farko a duniya da aka fara gwada maganin Coronavirus a jikinta"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?