LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Sha'awar juna ce ta kama mu muka yi lalata - Wanda yayi garkuwa da matar aure

- Yace bai yi amfani da kwaroron roba wajen saduwa da ita don da yardar matar yayi - Yayi garkuwa da matar auren ne amma yayin jiran mijinta ya biya kudin fansa, sai sha'awar juna ta kama su har suka yi lalata Wani mai garkuwa da mutane mai shekaru 27 mai suna Saidu Iliya da ke kauyen Gada Yeregi a karamar hukumar Lavun ta jihar Neja, 

ya bayyana yadda yayi lalata da wata mata mai matsakaicin shekaru. Iliya yayi garkuwa da matar ne kuma sai yayi lalata da ita yayin da yake jiran mijinta ya biya kudin fansa. Sa'ar shi ta kare ne a yayin da wata rundunar hadin guiwa ta 'yan sanda da 'yan sintirin da ke kauyen Vunu suka kama shi. A lokacin da aka tambayeshi ko ya yi amfani da kwaroron roba wajen lalatar da yayi da ita, 

sai yace, "banyi amfani dashi ba don da yardar juna muka yi ba fyade nayi mata ba." An gano cewa, a ranar 5 ga watan Maris ne wani Mohammed Sani da ke sansanin Fulani na Vunu da ke Luvun ya kai rahoton cewa wasu mutane dauke da makamai sun kai hari gidan shi inda suka sace matar shi. Jaridar Northern City News ta gano cewa masu garkuwa da mutanen sun bukaci naira miliyan 10 na kudin fansa amma daga baya sai suka sasanta a naira dubu dari shida.

An kama Iliya kuwa a ranar 8 ga watan Maris yayin da yaje karbar kudin fansa. Iliya ya bayyana cewa, "Tunda mu biyu ne a kebance, sai sha'awar juna ta kama mu inda na nemi kwanciya da ita. Zai yuwu bata son bata min rai ne da zai sai in kasheta. "Ban tirsasata ba wajen kwanciyar. Da kanta ta mika min kanta a yayin da nake jiran kudin fansa." Kakakin rundunar 'yan sandan, 

Wasiu Abiodun, ya ce wanda ake zargin ya amsa laifinsa. Ya bayyana cewa jami'an sun kubutar da matar ba tare da ta samu rauni ba. Sun samu bindiga daya a tare dashi sannan bayan kammala bincike za a mika shi gaban kotu.


LATSA NANπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y


KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 
Post a comment

0 Comments