--
Donald Trump ya yi gwajin Coronavirus bayan ya hadu da wani Mai dauke da cutar

Donald Trump ya yi gwajin Coronavirus bayan ya hadu da wani Mai dauke da cutar



Shugaban kasar Amurka, Donald J. Trump ya yi gwaji domin gano ko cewa ya na dauke da cutar nan ta Coronavirus da ta zama annoba yanzu a kasashen Duniya.
Kamar yadda labari ya zo mana daga gidan talabijin na Fox News, har yanzu ba a fito da sakamakon wannan gwaji da shugaban na Amurka ya yi ba tukuna.
Fox News sun fitar da wannan rahoto ne a Ranar Asabar, 14 ga Watan Maris, 2020. Ana sa ran ba da dadewa ba, Duniya za ta san halin da Donald Trump ya ke ciki.

A lokacin da ya gana da Manema labaran da ke cikin fadar shugaban kasa a karshen makon nan, Mai girma Donald Trump ya shaida masu cewa garau ya ke jin kansa.
Shugaban Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa jikinsa bai yi wani zafi ba. Zafin jiki da tari su na cikin alamomin wannan cuta ta Coronavirus da ba a gane kanta ba.

Donald Trump ya yi gwajin ne a sakamakon haduwar da ya yi da Tawagar shugaban kasar Brazil, Jair Bolsonaro, da wasu manyan jami’an gwamnatinsa a makon jiya.

Babban Sakataren yada labarai na gwamnatin Jair Bolsonaro watau Fabio Wajngarten ya na cikin wadanda su ka hadu da Trump, kuma yanzu haka ya na dauke da cutar.

Wannan na zuwa ne jim kadan bayan shugaban kasar ya nemi mutanensa su komawa Ubangiji game da wannan mummunar cuta da ta kashe mutane 5, 000 a Duniya.
Idan ba ku manta ba dai, kasar Mexico ta fara tunanin rufe iyakokinta da kasar Amurka a dalilin wannan cuta. Mexico ta na ganin hakan zai rage yaduwar annobar.
LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y


KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




0 Response to "Donald Trump ya yi gwajin Coronavirus bayan ya hadu da wani Mai dauke da cutar"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?