LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Dokar hana zirga-zirga a Kaduna: 'Yan sanda sun kama mutane 165 sun kuma kwace ababen hawa 205

- Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta kama mutane 165 da kuma ababen hawa 205 sakamakon kin bin dokar ta-bacin da gwamnatin jihar ta saka

- Kamar yadda kakakin rundunar 'yan sandan jihar ya bayyana, rundunar 'yan sandan da sauran cibiyoyin tsaro sun hada kai don tabbatar da jama'a sun bi dokar - A cikin mutane 165 da aka damke, akwai wasu malamai biyu wadanda suka ki bin dokar hana taro suka ja sallar jam'i a Unguwar Kanawa da ke Kaduna Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta kama mutane 165 da kuma ababen hawa 205 sakamakon karya dokar ta-bacin da aka saka a jihar don hana yaduwar cutar COVID-19.

Wannan na kunshe ne a takardar da kakakin rundunar 'yan sandan jihar, ASP Mohammed Jalige ya fitar a ranar Litinin.

Kamar yadda takardar ta bayyana, "Biyo bayan dokar ta bacin da aka saka a jihar Kaduna a ranar 27 ga watan Maris 2020 da kuma dokar gwamnatin tarayya ta nisantar taruka don hana yaduwar cutar coronavirus, rundunar 'yan sandan jihar Kaduna karkashin jagorancin Kwamishinan 'yan sanda U.M Muri, tare da hadin guiwar sauran cibiyoyin tsaro, suna tabbatar da cewa an bi dokar.


"Jami'an rundunar tare da sauran hukumomin tsaro sun kama mutane 165 tare da ababen hawa 205 da suka hada da motoci da babura. Akwai malaman addini biyu da aka damke bayan sun ki bin dokar hana taro." Ya yi kira ga jama'a da su kasance masu bin doka, kiyaye dokokin hana yaduwar cutar da kuma ci gaba da zama a gida don tabbatar da lafiyar jama'ar jihar, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

LATSA NANπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP  https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1YKU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 
b

Post a comment

0 Comments