LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Babbar magana: An nade kafet din Masallacin Harami a Saudiyya saboda coronavirus

A yayinda rahotanni suka bayyana cewa an kara samun karuwar mutane a kalla 19 da suka kamu da kwayar cutar corona a kasar Saudiyya, shugaban masallatan Haramain da ke birnin Makkah da Madinah, Sheikh Sudais, ya bayar da umarnin a nade shinfidun da ke cikin masallatan. 


 A wata sanarwa da shafin masallatan ya fitar a shafinsa na dandalin sada zumuntar 'facebook' (Haramain Sharifain), an bayyana cewa za an maye gurbin kafet din masallatan da wasu layuka da aka zana a kan tayil din masallatan. A sanarwar da aka wallafa a shafin, an ga hotunan wasu ma'aikatan masallatan na nade kafet din tare da zana sabbin layukan

Nade shimfidun masallatan na daga cikin matakan kiyaye wa da kare yaduwar kwayar cutar coronavirus da ke cigaba da yaduwa a sassan duniya. A cikin makon jiya ne hukumomin kasar Saudiyya suka sanar da rufe masallatan Harami da dakatar da aikin Umrah sakamakon bular annobar kwayar cutar corona.


LATSA NANπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP  https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y


KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 
Post a comment

0 Comments