LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

A karshe; Shugaba Buhari na wasa ya gabatar da jawabi ga 'yan Najeriya a kan coronavirus

Obinna Simon, wani dan Najeriya mai wasan barkwanci da ke matukar kama da shugaban kasa, Muhammadu, ya saki wani jawabi ga 'yan kasa inda a cikinsa ya yi magana a kan bullar annobar kwayar cutar coronavirus. Fitaccen mai wasan barkwancin, wanda aka fi sani da 'MC Tagwaye', 

ya saki jawabin ne a daidai lokacin da 'yan Najeriya ke cigaba da guna-guni a kan jinkirin da shugaba Buhari ke yi wajen gabatar da jawabi ga 'yan kasa a kan annobar coronavirus. Kamar yadda ya saba yin magana cikin kwaikwayon muryar Buhari, MC Tagwaye ya bukaci 'yan Najeriya su mayar da hankali wajen biyayya ga hanyoyin dakile yaduwar COVID-19. A cikin sakon faifan bidiyon mai tsawon dakika 140 da ya wallafa a shafinsa na 'Tuwita' 

(@MC_Tagwaye), ya ce, "shugaba Buhari ya hana dukkan jami'an gwamnati fita kasashen waje tare da daukan matakan dakile yaduwar kwayar cutar corona a fadin kasa. 

MC Tagwaye Source: Twitter "Dukkan kasashen duniya sun dauki matakan ganin cewa kwayar cutar ba ta cigaba da yaduwa a kasashensu ba. An dauki mataki a kan cutar ne ba don a takurawa jama'a ba, sai don a karesu daga kamuwa da ita. "Najeriya, kamar sauran kasashen duniya, ta dauki matakai daban-daban domin dakile kwayar cutar corona. Matakan sun hada da; 

"Haramtawa jami'an gwamnati fita kasashen ketare da kuma hana jirage daga wasu kasashen duniya sauka a Najeriya. Bayan an dauki wasu sauran matakai a cikin gida domin hana kwayar cutar uaduwa." Kalli faifan bidiyon: LATSA NANπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP  https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y


KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 
Post a comment

0 Comments