--
Covid-19: Iran ta yi watsi da tallafin Amurka

Covid-19: Iran ta yi watsi da tallafin Amurka

Shugaban addini a Iran Ayatollah Khamenei ya yi watsi da bukatar Amurka na tallafa wa kasarsa wajen yaki da coronavirus.
A wani jawabi da ya yi a talabijin, Ayatollah Khamenei ya bayyana cewa Amurka abokiyar gaba ce ga Iran kuma ya yi tsokaci kan wani batu da babu tabbas da ke cewa Amurka ce ta kirkiro annobar Covid-19.
Ya bayyana cewa duk da ba shi da tabbacin Amurka ce ta kirkiro annobar, amma babu wanda zai amince da Amurka ta kawo masa tallafin magani.
Ya ce ''akwai yiwuwar maganin da Amurka za ta bayar kan iya kara baza cutar''.
Wasu daga cikin jami'an gwamnatin ta Iran sun zargi Amurkar da 'munafunci' inda suka ce Amurkar ta ki cire takunkuman da ta saka wa kasar amma kuma ta wani gefe tana neman ta taimaka mata wajen yaki da coronavirus.



LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP  https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y


KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




0 Response to "Covid-19: Iran ta yi watsi da tallafin Amurka"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?