--
An samu karin masu cutar Coronavirus 10 a Najeriya, 3 a Abuja

An samu karin masu cutar Coronavirus 10 a Najeriya, 3 a Abuja

Ministan lafiya, Dakta Osagie Ehanire, ya bayyana cewa an samu karin mutane 10 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya. Ministan ya bayyana hakan ne a shafinsa na Tuwita ranar Asabar, 21 ga watan Maris, 2020. Yayinda bakwai aka samu a Legas, sauran ukun na birnin tarayya Abuja. Yanzu dai akwai jimillar masu cutar 22 a Najeriya kuma an sallami biyu da suka samu sauki,

Yace “Najeriya ta samu sabbin mutane 10 da suka kamu da cutar Coronavirus a Legas da Abuja. A yanzu haka akwai jimillar mutane 22 a Najeriya: Lagos 16, FCT 3, Ekiti 1 da Ogun 2.An sallami biyu.“ “Dukkansu yan Najeriya ne, 9 sun dawo daga kasar Faransa, Holan, Kanada, Spain da Ingila, daya ya kwasa ne daga wani daga cikinsu.“ “Wadanda ke Abuja ana jinyarsu a asibitin koyarwan jamiar UNIABUJA.“

“Wadanda ke Legas kuma ana jinyarsy a asibitin cututtuka a Legas.“ LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP  https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y


KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




0 Response to "An samu karin masu cutar Coronavirus 10 a Najeriya, 3 a Abuja"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?