Kutallata Hajarku Afarashi Maisuki, ________Mujallar BZGLOBALSERVICE.COM.NG________ Mujalla Ce Dake Watsa Labarai, Da Rohotanni, Labaran Nishadi, Bincike, Fadakarwa, Ilmantarwa Acikin Harshen Hausa, Kuma Acikin Awanni 24Hours Babu Qaqqautawa, Maziyartan Shafinmu Akowace Rana Basa Gaza Akallah Mutane Dubu biyar 5,000 Views Shafinmu Ya Shirya Tsaf Domin Karbar Tallace Tallace Daga Gareku Ma'abota Ziyartar Shafinmu Tallata Hajarka Adan Karamin Farashin Daya Fara Daga N1,000 Domin Bada Tallah Ko Qarin Bayani, Kutuntubemu Kaitsaye Ta Wadannan Numbobin: Kira: +2348133888333 Whatsapp: +2349066633320 Turo Mana Saqo Ta Adreshin Email: zaidusuleiman47@gmail.com "Colour"
 • LABARAN YAU

  Kutallata Hajarku Afarashi Maisuki,

  ________Mujallar BZGLOBALSERVICE.COM.NG________
  Mujalla Ce Dake Watsa Labarai, Da Rohotanni, Labaran Nishadi, Bincike, Fadakarwa, Ilmantarwa Acikin Harshen Hausa, Kuma Acikin Awanni 24Hours Babu Qaqqautawa, Maziyartan Shafinmu Akowace Rana Basa Gaza Akallah Mutane Dubu biyar 5,000 Views

  Shafinmu Ya Shirya Tsaf Domin Karbar Tallace Tallace Daga Gareku Ma'abota Ziyartar Shafinmu Tallata Hajarka Adan Karamin Farashin Daya Fara Daga N1,000 Domin Bada Tallah Ko Qarin Bayani, Kutuntubemu Kaitsaye Ta Wadannan Numbobin: Kira: +2348133888333 Whatsapp: +2349066633320 Turo Mana Saqo Ta Adreshin Email: zaidusuleiman47@gmail.com

  Latsa Koren Hoton Dake Qasa Domin Sauke Manhajar Labari Awayarka Ta Hannu Kyauta

  Friday, March 6, 2020

  An dage auren Suleiman Panshekara da masoyiyarsa 'yar Amurka

  Auren masoyan Instagram da za a yi a watan Maris din nan tsakanin Sulaiman dan Panshekara da ke Kano da kuma Jeanine Sanchez an dage shi har sai baba ta gani. An dage auren Sulaiman Panshekara da masoyiyarsa Jeanine Sanchez mai shekaru 46 ne saboda hatimin shiga Amurka da aka haramtawa ‘yan Najeriya. Da farko dai, an saka ranar auren Sulaiman Panshekara da baturiyar kasar Amurka da ta biyosa har Najeriya. Amma kuma an dage auren ne sakamakon haramtawa ‘yan Najeriya visa da aka yi ta shiga kasar Amurka.

  Baturiyar budurwar Sulaiman kuma amarya Jeanine, za ta nemi wasu halastattun hanyoyin mayar da angonta kasar Amurkan kafin a daura auren. A yayin tattaunawa ta wayar tafi da gidanka tsakanin jaridar Daily Trust da mahaifin ango Sulaiman, yace za a sanar da sabuwar ranar auren ne bayan Sanchez ta samo wasu hanyoyin samuwar takardar komawar dan sa Amurka. 

  Sulaiman mai shekaru 26 da Sanchez mahaifiyar yara biyu, sun fara soyayya ne a kafar sada zumuntar zamani ta Instagram kusan shekara daya da ta gabata. Ta ziyarcesa a Panshekara a watan Janairu kuma ta bukaci aurensa tare da tafiya da shi kasar Amurka. 

  An dage auren Suleiman Panshekara da masoyiyarsa 'yar Amurka Source: UGC 

  Isa yana aji biyu ne a jami’ar Yusuf Maitama Sule da ke jihar Kano. Tuni kuwa ya nuna amincewarsa na tafiya kasar Amurka don kammala karatunsa tare da gina soyayyar aure da masoyiyarsa baturiyar Amurka. Kamar yadda mahaifin angon yace, “Ba za a yi auren a watan Maris ba kamar yadda aka tsara da farko, saboda sabbin tsare-tsaren gwamnatin kasar Amurka na hana ‘yan Najeriya hatimin shiga kasar. Amma kuma matar na iya bakin kokarinta wajen samo hanyar samuwar takardun zaman Sulaiman a matsayin dan kasar. Bayan ta kammala kuwa za a saka sabuwar ranar biki

  ” Idan za a tuna, mahaifin angon ya tuntubi hukumar tsaro ta faraen kaya don hada kai da abokanta na CIA da FBI don karfafa bincike a kan sirikarsa. A yayin da aka tambayi dan sandan mai murabus, ya ce ana ci gaba da bincike har yanzu. Ya ce iyalansa sun kosa lokacin da burin Sulaiman zai cika na auren rabin ransa baturiyar kasar Amurka.


  LATSA NANπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y

  KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  KAYI TAMBAYA ANAN KOKA FADI RA'AYINKA AKAN ABINDA MUKEYI

  Item Reviewed: An dage auren Suleiman Panshekara da masoyiyarsa 'yar Amurka Rating: 5 Reviewed By: Admin
  AIKA LABARI