--
Bankuna 7 da Buhari zai ciwo bashin $22.7bn da majalisa ta bashi dama

Bankuna 7 da Buhari zai ciwo bashin $22.7bn da majalisa ta bashi dama

Bayan ganawar sirri sakamakon sabanin da aka fara samu a zauren majalisa, Majalisar dattawan tarayya ta baiwa shugaba Muhammadu Buhari daman karbo bashin $23bn (dala bilyan 22,798,446,773).

Shugaba majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis bayan gajeren mujadalan da akayi kan hakan.

Yayinda ake muhawara kan lamarin, shugaban marasa rinjaye, Eyinnaya Abaribe, ya gargadi majalisar kan baiwa shugaban kasa daman karbo bashin duka kudaden a lokaci guda.

Ya bada shawaran cewa a yi muhawara kan ayyukan da zaa karbo bashi kansu daya bayan daya. Amma shugaban majalisar datawa ya bayyana rashin amincewarsa da hakan.

Bayan haka sai aka fara tafka muhawara kan lamarin har aka fara samun sabani kuma haka ya tilasta yan majalisar saka labule.

Za ku tuna cewa a 2019, shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci karbo rancen kudi daga kasar waje lokacin Bukola Saraki amma suka hanashi.

Kimanin kashi 70 cikin 100 na bashin zai zo ne daga bankin kasar Sin yayinda za a karbo sauran daga bankin duniya da sauransu.


Ga jerin wurare 7 da Buhari zai karbo bashi da adadin da za a karbo wurinsu

1. Bankin shiga da fice na kasar Sin ($17bn)

2. Bankin Duniya ($2.95bn)

3. Bankin cigaban Afrika ($1.88bn)

4. Bankin cigaban Musulunci ($110m)

5. Hukumar hadin kai da kasashen waje na kasar Japan ($200m).

6. Bankin cigaban kasar Jamus ($20m)

7. Hukumar cigaban kasar Faransa ($480m


Bankuna 7 da Buhari zai ciwo bashin $22.7bn da majalisa ta bashi dama


LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y

KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




0 Response to "Bankuna 7 da Buhari zai ciwo bashin $22.7bn da majalisa ta bashi dama"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?