\ Shehu Sani ya roka wa Sarki Sanusi gafara a wajen Ganduje - BZGLOBALSERVICE.COM.NG Shehu Sani ya roka wa Sarki Sanusi gafara a wajen Ganduje - BZGLOBALSERVICE.COM.NG
Kutallata Hajarku Afarashi Maisuki, ________Mujallar BZGLOBALSERVICE.COM.NG________ Mujalla Ce Dake Watsa Labarai, Da Rohotanni, Labaran Nishadi, Bincike, Fadakarwa, Ilmantarwa Acikin Harshen Hausa, Kuma Acikin Awanni 24Hours Babu Qaqqautawa, Maziyartan Shafinmu Akowace Rana Basa Gaza Akallah Mutane Dubu biyar 5,000 Views Shafinmu Ya Shirya Tsaf Domin Karbar Tallace Tallace Daga Gareku Ma'abota Ziyartar Shafinmu Tallata Hajarka Adan Karamin Farashin Daya Fara Daga N1,000 Domin Bada Tallah Ko Qarin Bayani, Kutuntubemu Kaitsaye Ta Wadannan Numbobin: Kira: +2348133888333 Whatsapp: +2349066633320 Turo Mana Saqo Ta Adreshin Email: bzglobalservicelabari@gmail.com "Colour" <#20124d>
 • LABARAN YAU

  Friday, March 6, 2020

  Shehu Sani ya roka wa Sarki Sanusi gafara a wajen Ganduje

  Tsohon dan majalisar dattijai, Sanata Shehu Sani ya roki Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano a kan ya yafe wa Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II a kan duk wani abinda ya yi ba dai-dai ba. Sani ya sanar da hakan ne a yau Juma’a a wallafa da yayi a shafinsa na Twitter. Ya yi kira ga Gwamna Ganduje a kan “ya yi yafiya, 

  ya kuma manta da abinda ya wuce ya kyale sarki Sanusi II”. Ya kara da kira ga gwamnan da ya sani cewa mulki na juyi ne kuma watarana zai iya bukatar taimakon Sarkin. Sarkin Kano din dai na fuskantar sabuwar tuhuma ne daga hukumar sauraron koke da yaki da rashawa ta jihar Kano, a kan zargin damfarar naira biliyan 2.2 na fili.

   Shehu Sani ya roka wa Sarki Sanusi gafara a wajen Ganduje Source: Twitter 

  Sarkin mai matsayi na farko zai bayyana a gaban kungiyar masu bincike ne ta hukumar a jiya amma sai bai samu zuwa ba. Ya bukaci a saka masa wata rana daban don zuwa amsa tambayoyinsu. 

  Amma kuma a yau Juma’a ne hukumar ta jaddada cewa tilas ne sarkin ya bayyana gabanta don amsa tambayoyinta a ranar 9 ga watan Maris din 2020. 

  Sanannen abu ne idan aka ce akwai Baraka tsakanin gwamnan da Sarki Sanusi kuma hakan yasa aka fara masa sabuwar tuhumar bayan ta farko din da ta tarwatse a kotu. Ba wannan bane karon farko da masarautar Kano din ake bincikarta tun bayan da Malam Muhammadu Sanusi II ya hau karagar mulkinta a 2014. 

  Hukumar binciken ta binciki Sarki Sanusi a kan abinda ta kwatanta da kisan kudi ba bisa ka'ida ba har na naira biliyan hudu. Amma kuma daga baya ta dakatar da binciken. Idan za mu tuna, wata babbar kotun tarayya da ke zama a Kano a watan da ta gabata, ta yi watsi da rahoton hukumar inda ta zargi sarkin da damfarar naira biliyan 3.4 daga cikin kudin masarautar. 


  LATSA NANπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y

  KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  KAYI TAMBAYA ANAN KOKA FADI RA'AYINKA AKAN ABINDA MUKEYI

  Item Reviewed: Shehu Sani ya roka wa Sarki Sanusi gafara a wajen Ganduje Rating: 5 Reviewed By: Admin