--
An bayyana shirin tsohon sarki Sanusi II na gaba bayan tube rawaninsa

An bayyana shirin tsohon sarki Sanusi II na gaba bayan tube rawaninsa

- Sananne a kafar yada labarai, Dele Momodu a ranar Litinin ya kai wa tubabben sarkin Kano, Sanusi Lamido ziyara a Legas - A yayin ziyarar da Momodu ta kai wa tsohon gwamnan babban bankin Najeriya din, 

ya ce sam wannan hukuncin na gwamnatin jihar Kanodin bai bata wa basaraken rai ba - Sananne a kafar yada labarai ya bayyana cewa, a halin yanzu Sanusi na kokarin ganin yadda zai amfani al'umma ne da gogewarsa Sananne a kafar yada labarai, Dele Momodu a ranar Litinin ya kai wa tubabben sarkin Kano,

Sanusi Lamido ziyara a Legas. Sanusi, wanda ya samu 'yancinsa bayan wata babbar kotu a Abuja ta yanke hukuncin gaggawar sakinsa, a halin yanzu yana jihar Legas. A yayin ziyarar da Momodu ta kai wa tsohon gwamnan babban bankin Najeriya din, ya ce sam wannan hukuncin na gwamnatin jihar Kano bai bata wa basaraken rai ba.

Sananne a kafar yada labarai ya bayyana cewa, a halin yanzu Sanusi na kokarin ganin yadda zai amfani al'umma ne da gogewarsa. Idan zamu tuna, Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, a cikin sa'o'i 48 bayan tubewa tsohon sarkin Kano din rawani, 

ya bashi mukamai har biyu a jihar. A shafinsa na twitter, Momodu ya rubuta: "Na dau lokaci mai inganci da amfani a tare da tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II da wannan yammacin. Yana cike da burin ci gaba kuma bai nuna damuwarsa ba a kan abinda ya faru. "Ya zabi ci gaba da ayyukan da zasu amfani al'umma da gogewarsa hadi da iliminsa. Ina masa fatan alheri." 

LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y


KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




0 Response to "An bayyana shirin tsohon sarki Sanusi II na gaba bayan tube rawaninsa "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?