--
Biloniya dan China zai tallafa wa Afirka kan Coronavirus

Biloniya dan China zai tallafa wa Afirka kan Coronavirus


Wani hamshakin mai arziki dan kasar China kuma mamallakin Gidauniyar Jack Ma, ya sanar da bai wa nahiyar Afirka tallafi na kayayyakin da ake amfani da su a asibiti kan cutar Covid-19 har 20,000 ga kowace kasa.
Gidauniyar ta sanar da hakan ne a shafinta na Twitter a ranar Litinin, a yayin da kasashen duniya da dama ke ci gaba da fafutukar hana yaduwar cutar.
A sanarwar gidauniyar, ta ce Afirka za ta iya kare kanta daga coronavirus idan ta dauki mataki.
Kayayyakin sun hada da takunkumin rufe fuska 100,000 da rigunan da ma'aikatan lafiya ke sa wa don kare kansu da sauran kayan da ake amfani da su wajen kula da masu cutar.

Sanarwar ta ce: "Ba za mu iya kawar da kanmu daga hadarin da Afirka ke fuskanta ba, mu dauka cewa wannan nahiya mai mutum biliyan 1.3 za ta tsira a wannan iftila'i ba.
"Duniya ba za ta zuba ido ta ga mummunan abin da zai iya faruwa a Afirka ba kan wannan annoba ta Covid-19.
"Za mu iya daukar matakan kariya yanzu mu kuma shirya kafin lokacin faruwar wani abu, saboda Afirka za ta iya amfana da koyon darussa daga wasu kasashen da bala'in ya shafa."
Kazalika Gidauniyar ta Jack Ma ta ce nan ba da dadewa ba za ta fara aiki da cibiyoyin lafiya a Afirka don ba su horo ta intanet, na yadda ake kula da masu jinyar cutar Covid-19.
A jumlace Afirka za ta samu kayayyakin har miliyan 1.1 da suka kunshi takunkumin fuska miliyan shida da rigunan da ma'aikatan lafiya ke sa wa don kare kansu 60,000 da gilashin rufe fuska, kuma za a kai kayan birnin Addis Ababa na kasar Habasha ne.
Firai Ministan Habasha Abiy Ahmed Ali ne zai jagoranci rarraba kayayyakin tare da aike wa sauran kasashen.
A karshe sanarwar ta ce, wannan annoba tana kara yaduwa kuma tana wuce duk yadda aka tsammace ta.
Cutar coronavirus dai na ci gaba da yaduwa a kasashen dubiya daban-daban, sai dai har yanzu ba ta yi barna sosai a Afirka ba kamar sauran nahiyoyi.
LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y


KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




0 Response to "Biloniya dan China zai tallafa wa Afirka kan Coronavirus"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?