Yauwa, mun godewa Allah da CBN zasu samar da shirin musanyar tsohon kuɗi zuwa sabo ga mutanen da suke karkara ko kuma suke da ƙarancin bankuna.
A cikin abubuwan da suka sake dubawa akwai:
1. Baza a bawa mutum É—aya sabon kuÉ—i sama da N10,000 ba a hannu sai dai a karbi tsohon a tura masa zuwa asusun banki idan sun wuce haka.
2. Idan mutum bashi da asusu to za karbi bayanansa a take a buÉ—e masa sannan a saka masa kuÉ—insa a ciki.
3. Akwai takardun N100, N50, N20, N10, N5 wadda idan mutum bai samu waÉ—anda aka canza ba, za a sauya masa da waÉ—annan.
4. Wakilan da zasu samar suna da damar karɓar tsofin kuɗi su baka sabo kuma kyauta ne, saidai abinda ake cira idan mutum zai cire kuɗinsa koda da kansa ne.
5. Daga baya wakilan da suka saka akan aikin zasu dinga mayarwa da banki tsohon kuÉ—in. Kamar yadda suka ce, wannan shiri ne da za'a aiwatar a dukkan kananan hukumomi na jihohin Najeriya.
Allah Ya kare al'ummar Sa da asarar dukiyar su, Ya kuma wadata mu, Amin