--
Anbude Shafin daukar ma'akatan Zaben Na Shakarar 2023 (Inec Ad-Hoc Staff Recruitment) Mai Sha'awa yaje yacike Anbude Shafin Yanar Gizon Yanzu Haka

Anbude Shafin daukar ma'akatan Zaben Na Shakarar 2023 (Inec Ad-Hoc Staff Recruitment) Mai Sha'awa yaje yacike Anbude Shafin Yanar Gizon Yanzu Haka



Hukumar zabe mai zaman kanta INEC zata dauki sabbin ma'aikatan wucin gadi na zaben da zaa gudanar 2023 za'a bude manhajar yanar gizon daukar ma'aikatan da safiyar yau laraba karfe 8:00 14 ga watan satumba 2022 


Ku tabbatar kun cike dukkan ka'idojin da hukumar ta gindaya domin samun nasarar cin gajiyar shiga aikin. 


Dalilai barkatai da suke hana mutanan mu samun duk wani abu da gwamnatin tarayya ta bude, Abu na farko shine rashin karanta sharudan dake cikin yanar gizon wanda hukumar ta gindaya ,ga lambar da zakuyi magana da ita ta WhatsApp 08097206320 domin sanya muku abubuwan da suka dace da yardar Allah mutum zai samu nasara.


Wurin neman aikin ko cike wani abu daban da gwamnatin tarayya ta bude ba'a bukatar mutum yayi gagawa abu a hankali wurin cikewa, ka tabbata abun da suka tambaya kasa a wurin kada ka sanya musu abun da basu bukata ba. 



Karanta ka'idojin yana da mutukar mahimmanci ga mai nema domin ta nan ne kadai zaka iya gano abubuwan daya dace ya nema dasu,dole mu bi a hankali mu natsu wurin karanta bayanai da hausa ko da turanci duk abun daka gani ba kayi tambaya ga wanda kasan ya fika ido a harkar abu mafi dacewa ga wanda ba zasu yi cikawa ba suyi magana ta WhatsApp 08097206320 nayi imani da Allah zai muku aiki bisa Amana Kuma zai bi muku dukkan ka'idojin da aka gindaya .


Shawara ga masu nema aikin ko wani abu daban. 👇


Ku sane wani bawa bai isa ya baku abun da Allah bai kaddara ba, kada kace ka dade kana nema baka samu ba ka cigaba da nema ka sanyawa zuciyarka cewa Allah ne kadai zai kaddara ka samu ko rashin samun. 


komai lokaci ne a wannan rayuwar da kuke gani idan lokacin samun aikin ka baiyi ba wallahi tallahi ko shugaban kasa ne ya haifi ka ba zaka samu ba, idan ko lokacin samun aikin ka yayi zaka raina kaddarar silar samun aikin ka. 


Komai zamuyi mu nemi shawarar iyaye don su sanya mu acikin addo'in su Allah ka cigaba da ciyar damu alheri. 



Ga masu sha'awa sai su yi rijista ta wannan hanyar yanar gizo : http://www.inecnigeria.org


©️Ahmed El-rufai Idris

Kaduna State Coordinator Zumunta Youth Awarenesses forum 🤝

0 Response to "Anbude Shafin daukar ma'akatan Zaben Na Shakarar 2023 (Inec Ad-Hoc Staff Recruitment) Mai Sha'awa yaje yacike Anbude Shafin Yanar Gizon Yanzu Haka"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?