--
YANZU-YANZU: Babbar Kotu A Kaduna Ta Wanke Shaikh Zakzaky Ta Kuma Bada Umurnin A Sake Shi yanzu batare da bata lokaciba,

YANZU-YANZU: Babbar Kotu A Kaduna Ta Wanke Shaikh Zakzaky Ta Kuma Bada Umurnin A Sake Shi yanzu batare da bata lokaciba,




Daga Ammar M. Rajab 


Babbar kotu a Kaduna ta bada umurnin a saki Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky da matarsa Malama Zeenatuddeen Ibrahim tare da wanke su daga dukkanin zarge-zargen da gwamnatin Kaduna ke musu guda takwas. 


Kotun ta bada umurnin ne a zamanta na yau Laraba 28 ga watan Yulin 2021 daidai da 18 ga watan Zulhijjah, 1442 a yayin yanke shari'ar da aka kawashe tsawon shekaru biyu ana yinta. 


Mai shari'a Gideon Kurada ne ya yanke hukuncin.

0 Response to "YANZU-YANZU: Babbar Kotu A Kaduna Ta Wanke Shaikh Zakzaky Ta Kuma Bada Umurnin A Sake Shi yanzu batare da bata lokaciba, "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?