--
Kalli Hotunan 'Ɗan Sanda' Da Sojoji Suka Kama Da Harsashi 220 Da Gurneti a Borno

Kalli Hotunan 'Ɗan Sanda' Da Sojoji Suka Kama Da Harsashi 220 Da Gurneti a Borno


Dakarun sojojin Nigeria na Operation Hadin Kai sun kama wani da ake zargi da laifi, Ebenezer Ojeh, wanda ya yi ikirarin cewa shi dan sanda ne mai mukamin saja dauke da harsasai da gurneti a jihar Borno, 


The Cable ta ruwaito. PRNigeria ta ruwaito cewa Dakarun Sojoji na 154 Battalion Ngamdu karkashin jagorancin mukadashin kwamanda Manjo D.Y. Chiwar ne suka kama wanda ake zargin a hanyar Maiduguri zuwa Damaturu. 


Ta yaya aka kama wanda ake zargin? Wani majiya daga sashin tattara bayanan sirri ya ce: 


"An kama Ebenezer Ojeh ne a shingen binciken jami'an tsaro saboda yanayin alamun rashin gaskiya da aka lura da shi tun lokacin da ya hau motar haya ta Borno Express domin zuwa Abuja. 


"Bayan an bincika jakarsa, an gano kimanin harsashi 220 masu tsawon 7.62mm, gurneti na hannu guda daya, karamar wuka da wasu kayayakin. 


"Yayin da sojoji ke masa tambayoyi, Ojeh ya yi ikirarin cewa shi jami'in rundunar yan sandan Nigeria ne a sashi na musamman ta SWAT a jihar Rivers. 


"Duk da cewa unifom da abin suna da ke hannunsa na dauke da sunan wani Saja Ebenezer Ojeh mai lamba 456647, ba mu riga mu tabbatar ko shi wanene ba da abin da ya kawo shi Borno tunda ya yi ikirarin cewa a jihar Rivers ya ke aiki." 


Wani majiyar ta sojoji ta shaidawa The Cable cewa ana zargin dan sandan bogi ne. Majiyar ta ce: "Bai kamata ya yi tafiya da makamai ba. 


Abin zargi ne. Babu dan sandan da aka bawa izini ya rika tafiya da ko da harsashi daya ne. Kuma da aka tsayar da shi, ya yi kokarin tserewa kafin aka taro shi." 


An mika wanda ake zargin da kayayyakin da aka kama shi da su ga hedkwata ta sector 2 na Operation Hadin Kai domin zurfafa bincike. 




0 Response to "Kalli Hotunan 'Ɗan Sanda' Da Sojoji Suka Kama Da Harsashi 220 Da Gurneti a Borno "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?