--
Kalli adadin makuden kudin da sabon kulob din Ahmed Musa zai dinga biyansa duk Shekara

Kalli adadin makuden kudin da sabon kulob din Ahmed Musa zai dinga biyansa duk Shekara


Fitaccen dan kwallon kafan Najeriya, Ahmed Musa ya samu wurin zama a sabuwar kungiyar kwallon kafa da ya koma Dan kwallon kafan mai shekaru 28 ya koma wata kungiyar kwallon kafa a kasar Turkiyya


kuma zai dinga samun N1bn a kowacce shekara Kungiyar kwallon kafan ta kasar Turkiyyan ta saka buri kan sabon zakaran da ta samu a wasannin nan gaba 


Istanbul, Turkiyya - Kyaftin din Super Eagles, Ahmed Musa ya sa hannu kan wata sabuwar harkalla da wata kungiyar kwallon kafa ta Turkiyya bayan kwashe watanni hudu da Kano Pillars. 


Kamar yadda Legit.ng ta gano, kungiyar kwallon kafan ta gabatar da matashin zakaran mai shekaru 28 a duniya bayan an yi masa gwajin lafiya. 


Babu shakka wannan makuden kudaden ne suka saka zakaran kwallon kafan ya kasance daya daga cikin 'yan kwallon kafa da yafi kowa samun kudi a duniya. 


Fitaccen dan wasan kwallon kafan ya shiga tsararrakinsa a yayin da yake kokarin farfadowa yayin da a bangaren Super Lig kuwa suke ta shirye-shiryen wasannin 2021-22. Ya bar kungiyar Al Nassr a shekarar da ta gabata 


Kafin komawarsa Turai, Musa ya bar kungiyar kwallon kafa ta Al Nassr dake Saudi Arabia a watan Oktoban da ya gabata kuma yayi yunkurin komawa kungiyar West Bromwich Albion a watan Janairun da ta gabata amma hakan ya gagara. 


Source: Legit

0 Response to "Kalli adadin makuden kudin da sabon kulob din Ahmed Musa zai dinga biyansa duk Shekara "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?