--
Mata sun hada fada tsakanin ISWAP da bangaren Shekau, an sheke 'yan ISWAP masu tarin yawa

Mata sun hada fada tsakanin ISWAP da bangaren Shekau, an sheke 'yan ISWAP masu tarin yawa




Gagarumar arangama tsakanin Boko Haram bangaren Abubakar Shekau da mayakan ISWAP ya kawo ajalin mayakan ISWAP masu tarin yawa, HumAngle ta ruwaito. Gagarumin fadan ya faru ne a yankinsa tsakanin iyakar Nijar da Najeriya. 


Al-Thabat, wata kafar yada labarai mai alaka da al-Qaida ta bayyana. A wata takarda da Al-Thabat ta fitar, ta ce Jama’at Ahl as-Sunnah lid-Da’wah wa’l-Jihad wacce aka fi sani da Boko Haram ta halaka mayakan ISWAP a wani kauye da ake kira da Sunawa tsakanin iyakar Najeriya da jamhuriyar Nijar. 


BBC ta ruwaito cewa an fara rikicin ne bayan ISWAP ta yi garkuwa da mata masu tarin yawa wadanda ke da alaka da Boko Haram. Babu bata lokaci kuwa Boko haram ta kai hari sansanin ISWAP din kuma ta ceto matan. 


A shekarar 2016 ne bangaren Boko Haram na Shekau ya rabe daga ISWAP kuma tun daga nan suke ta samun hargitsi tare da hayaniya. 


DAGA BZ NEWS 24/7

Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta: 

Facebook:https://web.facebook.com/bzlabari24 

Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: 

bzglobalservicelabari@gmail.com

0 Response to "Mata sun hada fada tsakanin ISWAP da bangaren Shekau, an sheke 'yan ISWAP masu tarin yawa"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?