--
Yanzu yanzu: Majalisar dattijai ta ba da umarnin kama dukkan masu gudanar da NDDC kan badakalar biliyan N2.6b

Yanzu yanzu: Majalisar dattijai ta ba da umarnin kama dukkan masu gudanar da NDDC kan badakalar biliyan N2.6b


Kwamitin Majalisar Dattawa dake karbar koke-koken jama'a, da da'a da kuma gata sun ba da sammacin kame dukkan masu gudanar da Hukumar Raya Yankin Neja Delta (NDDC).


Shugaban Kwamitin, Sanata Ayo Akinyelure ya ba da wannan umarnin ne sakamakon gazawar da mahukunta suka yi don girmama gayyatar da kwamitin majalisar dattijai ya yi musu don yin bayanin yadda aka kashe zunzurutun kudin N2.6 biliyan wanda Gwamnatin Tarayya ta fitar.


Jaridar DAILY POST ta ruwaito cewa kwamitin majalisar dattijai wanda ya fara binciken zargin karkatar da kudaden tallafi na N2.6 biliyan yana da wahala a samu binciken hukumar NDDC.


Takardar karar wacce aka gabatar a gabanta ta Shugaban Hukumar ta NDDC, Mista Jackrich Sobomabo wanda ya dage kan cewa asusun da ya kamata a bayar a karkashin kulawar hukumar ta NDDC ta karkatar da shi.


Da yake magana bayan sammacin kamun, Mista Jackrich Sobomabo ya koka kan yadda ya sanya kokarinsa da dukiyar sa wajen gudanar da aikin sassaucin a gaban hukumar NDDC da ake zargi da karkatar da kudaden.


“An nada ni Shugaban sasantawa, amma lokacin da Gwamnatin Tarayya ta fitar da zunzurutun kudi Naira biliyan 2.6, sai shugabannin NDDC suka kashe kudin ba tare da sani na ba.


“Abin takaici ne cewa sun kasance masu kauracewa lokacin da kwamitin Majalisar Dattawa ya bukaci su zo su yi bayanin yadda aka kashe kudaden.


“Idan daga karshe suka zo suka yi bayani mai gamsarwa, zan kasance lafiya, amma dole ne su bayyana don bayanin yadda aka raba asusun.


Ya nuna kwarin gwiwa cewa Majalisar Dattawan Najeriya za ta hukunta wadanda suka aikata laifin.


DAGA BZ NEWS 24/7

Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta: 

Facebook:https://web.facebook.com/bzlabari24 

Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: 

bzglobalservicelabari@gmail.com

0 Response to "Yanzu yanzu: Majalisar dattijai ta ba da umarnin kama dukkan masu gudanar da NDDC kan badakalar biliyan N2.6b"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?