--
Korona 2.0: Za'a ji jiki a watan Janairu; NCDC ta gargadi 'yan Nigeria

Korona 2.0: Za'a ji jiki a watan Janairu; NCDC ta gargadi 'yan Nigeria



NCDC, cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa, ta ce 'yan Nigeria sun yi uwar watsi da matakan dakile yaduwar annobar korona 


Shuagaban NCDC ya ce 'yan Nigeria su shirya domin za'a fuskanc hauhawar alkaluman masu kamuwa da cutar korona daga satin nan Cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa a Nigeria (NCDC) ta yi gargadin cewa za'a sha wahala a cikin watan Janairu mai zuwa saboda hauhawar alkaluman masu kamuwa da cutar korona da za'a fuskanta. 


NCDC ta ce za'a fuskanci hauhawar alkaluman mutanen da kwayar cutar za ta harba saboda yadda jama'a suka yi burus da matakan kiyayewa yayin bukukuwan hutun da aka samu, kamar yadda The Nation ta rawaito. A cewar NCDC, makon da ya gabata ya kasance daga cikin mafi ban tsoro saboda tashin gwauron zabi da alkaluman mutanen da suka kamu da cutar ya yi. 


A saboda haka, cibiyar ta gargadi 'yan Nigeria tare da yi musu tunin cewa su shirya girbar abinda suka shuka tunda suka yi watsi da dukkan sharuda da matankan kiyayewa yayin hutun bukukuwan kirsimeti da karshen shekara. 


Darekta Janar na NCDC, Dakta Chikwe Ihekweazu, shine ya fadi hakan a Abuja yayin taron kwamitin PTF akan korona na ranar Talata. 


"Mun fuskanci sati mafi muni tun bayan barkewar annobar korona, amma sai gashi cikin makon da ya biyo bayansa, jama'a sun yi watsi da duk wasu matakan kiyayewa. "Ga hotuna da bidiyon taron jama'a a wurin shagulgulan biki suna ta yawo a dandalin sada zumunta, abin haushi da tayar da hankali. 


"Za'a ji jiki a watan Janairu, babu wani abin mamaki idan an fuskanci hauhawar alkaluman mutanen da zasu kamu da kwayar cutar korona sakamakon cudanya da saba ka'idojin da gwamnati ta gindaya," a cewarsa. 


 Source: Legit

Mtn Data Bonanza By Bz Global Services 🌐

1GB @N350 

2GB @N700

3GB @N1,050

4GB @N1,400

5GB @N1,750

Validity For 30Days

Hanyar Biya Bank Transfer Domin Siya Yanzu Kiramu Ta Number Waya 08133888333 Koka Aiko Sako Ta Whatsapp: 09066633320


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Korona 2.0: Za'a ji jiki a watan Janairu; NCDC ta gargadi 'yan Nigeria"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?