--
Karin bayani: Majalisar wakilai ta aika sammaci ga Buhari kan kisan Zabarmari

Karin bayani: Majalisar wakilai ta aika sammaci ga Buhari kan kisan Zabarmari


Daga karshe majalisar wakilai ta aika sammaci ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari domin ya gurfana a gabanta kan kisan Zabarmari - A yayin zaman majalisa a ranar Talata, 1 ga watan Disamba, zauren majalisar wakilan ya kaure da hayaniya yayinda yan majalisar suka sha bamban kan lamarin 


Sai dai kuma, an bukaci Shugaban kasar ya kaddamar da dokar ta baci a wasu yankunan kasar Bayan an kai ruwa rana, majalisar wakilai ta aika sammaci ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari akan kisan manoma 43 a garin Zabarmari da ke jihar Borno, jaridar Premium Times ta ruwaito. 



Yan majalisar sun yanke shawarar ne a ranar Talata yayinda suka aminta da wani jan hankali da Satomi Ahmed yayi na cewa hakan na da matukar muhimmanci. Da fari mun ji cewa hatsaniya ya kaure a majalisar wakilai kan wani kudiri da aka gabatar na neman a gayyato Shugaban kasa Muhammadu Buhari domin ya amsa tambayoyi a kan hauhawan rashin tsaro a kasar. 


A yayin zaman majalisar a ranar Talata, 1 ga watan Disamba, daya daga cikin yan majalisar ya gabatar da wata bukata na gayyatar shugaban kasar gaban majalisar dokokin tarayya. Amma sai lamarin ya tunzura wasu yan kashenin Buhari, don haka sai rashin jituwa ya gibta a tsakani, TVC ta ruwaito. 


Amma dai, bukatar neman Shugaban kasar ya kaddamar da dokar ta baci a yankunan arewa maso gabas da arewa maso yamma ya samu karbuwa a wajen yan majalisar. Daga nan sai shugabannin majalisar suka shiga wata ganawa domin yanke hukunci kan banbancin ra’ayi da aka samu game da bukatar. 


A baya mun ji cewa, biyo bayan kisan manoma 43 a jihar Borno wanda yan Boko Haram suka yi, an bukaci gwamnatin tarayya da ta duba yiwuwar sauya tsarin tsaro a Najeriya. 


Dr. Ahmad Lawan ya yi kiran ne a ranar Litinin, 30 ga watan Nuwamba, lokacin da ya jagoranci tawagar Shugaban kasa domin yi wa gwamnati da mutanen Borno jaje kan mummunan lamarin, jaridar The Sun ta ruwaito. 


A cewar Lawan, tsarin da ake dashi a kasa baya aiki, inda ya kara da cewa gwamnati na bukatar samun sabbin manufofi da kuma ganin yadda tsarin tsaron zai inganta. 



SOURCE: LEGIT

Mtn Data Bonanza By Bz Global Services 🌐

1GB @N350 

2GB @N700

3GB @N1,050

4GB @N1,400

5GB @N1,750

Validity For 30Days

Hanyar Biya Bank Transfer Domin Siya Yanzu Kiramu Ta Number Waya 08133888333 Koka Aiko Sako Ta Whatsapp: 09066633320


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Karin bayani: Majalisar wakilai ta aika sammaci ga Buhari kan kisan Zabarmari"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?