Da duminsa: Wasan buya ya kare, an kama Abdulrasheed Maina Nijar
Tuesday, 1 December 2020
Comment
Abdulrasheed Maina, tsohon shugaban kwamitin gyaran fansho, ya matsa layar zana a yayin da kotu ke nemansa a Najeriya - Bacewar maina ta sa kotu ta tsare Sanata Ali Ndume a gidan yari saboda shine ya karbi belin Maina bisa wasu sharudai Yanzu dai, karya ta kare, jami'an tsaro ma su bincike tare da hadun gwuiwar jami'an yaki da cin hanci sun sake cukume Maina a Nijar Jami'an binciken sirri da hadin gwuiwar na hukumar yaki da cin hanci sun kama Abdulrasheed Maina a Jamhuriyar Nijar a ranar Litinin.
Kamfanin dillancin labarai na PRNigeria ya ce an kama Maina a wani gari da ke cikin Jamhuriyar Nijar. A cewar majiyar jaridar, an samu nasarar kama Maina ne saboda kyakyawar alakar da ke tsakanin jami'an tsaron Najeriya da Nijar.
Wata babbar kotun gwamnatin tarayya da ke zamanta a Abuja ne ta sanar da janye belin Abdulrasheed Maina tare da bayar da umarin a kama shi duk inda aka gan shi.
A hukuncin da alkalin kotun, Okong Abang, ya zartar ranar Laraba, 25 ga watan Nuwamba, ya bayar da umarnin a sake kamo Maina ''duk inda aka gan shi".
Lauyan hukumar EFCC, Mohammed Abubakar, ya ce an bayar da belin Maina a kan kudi miliyan N500 da kuma mai tsaya masa; wanda dole ya kasance Sanata mai ci da zai ajiye miliyan N500 a kotu. Lauyan ya rubuta takardar korafi zuwa kotun inda a ciki ya zargi Maina da saba sharuda da ka'idojin belin.
Hukumar EFCC mai yaki da cin hanci ta gurfanar da Maina a gaban kotu bisa tuhuma goma sha biyu da ta shirya a kansa da kuma wani kamfani mai suna 'Common Input Properties & Investment Limited".
Bayan bawa hukumomin tsaro izinin kama shi, kotun ta bawa EFCC damar gurfanar da shi tare da tuhumarsa a kebance. Kafin Sanata Ndume ya karbi belinsa, Maina ya shafe tsawon watanni bakwai a gidan yarin Kuje. Bayan Maina ya cika bujensa da iska, kotu ta bayar da umarenin tsare Sanata Ndume a gidan yari na Kuje.
SOURCE: LEGIT
Mtn Data Bonanza By Bz Global Services 🌐
1GB @N350
2GB @N700
3GB @N1,050
4GB @N1,400
5GB @N1,750
Validity For 30Days
Hanyar Biya Bank Transfer Domin Siya Yanzu Kiramu Ta Number Waya 08133888333 Koka Aiko Sako Ta Whatsapp: 09066633320
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN:
KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK:
@TWITTER:
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765
0 Response to "Da duminsa: Wasan buya ya kare, an kama Abdulrasheed Maina Nijar"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?