--
Wata sabuwa: Matasa sun fasa shagon Mansura Isah a Kano, sun kwashe komai

Wata sabuwa: Matasa sun fasa shagon Mansura Isah a Kano, sun kwashe komai


Bata gari sun fasa shagunan mutane a garin Kano ciki har da shagon tsohuwar arumar Kannywood, Mansura Isah - Matasan wadanda suka fake da zanga-zangar EndSARS sun kwashe komai da ke ciki shagon jarumar 


Mansura ta bayyana cewa lamarin ya faru ne bayan sun hade kayayyakin dukka shagunansu a waje daya Wasu matasa da ake zaton bata gari ne a birnin Kano, sun kai mamaya shagon tsohuwar jarumar Kannywood, Mansura Isa da ke jihar. 


Bata garin sun fasa shagon nata da ke kan titin Filin Jirgin Sama daura da titin Ahmadiyya, inda suka yashe komai da ya ke ciki. Mansura wacce ta kasance mata ga fitaccen jarumin masana’antar, Sani Musa Danja, ce ta wallafa bidiyo da hotunan shagon da aka fasa mata a shafinta na Instagram. 


Ta wallafa a shafin nata cewa “Mun tattara kayanmu da ke ragowar sauran ofishinmu da ke unguwar Badawa zuwa wuri daya domin rage wa kanmu wahala akoda yaushe ta hanyar zirga-zirga daga wannan shagon zuwa wancan. Ofishinmu na @todays_life_foundation da ke Badawa layout, da shagonmu na daukar hoto @celebrityphotos2442 da kuma tsohon shagona da ke Audu Bako.


“Mun kwashe komai da ya ke shagon kama daga Takalma, jakunkuna, Firji, AC, Talabin da sauran kayayyaki daga tsoffin shagunan zuwa wannan sabon shagon domin mamallakan shagunan sun bukaci mu bar masu wajensu tunda ba za mu sake biyan haya ban a wata shekarar. Amma sunsace komai, basu bar ko takalmi daya ba. Sun kwashe komai da komai. Amma mun fawwala wa Allah komai. 


“Dama mun san mutane suna neman dama irin wannan ne domin su aikata mummunan laifuka, sun fake da zanga-zangar #EndSARS da kuma #EndInsecurity don su lalata dukiyoyin jama’a da rayukan mutane.” "Amma ina addu’a ga samun sabuwar Najeriya kuma muna yi wa kasarmu addu’an samun zaman lafiya. Alhamdulillah da kasancewa da lafiya da rayuwa.”



View this post on Instagram

We Vacate 2 of our shops to relocate to One shop, so that we won't have too much stress all the time, moving from one shop to another, our @todays_life_foundation office at Badawa layout, our @celebrityphotos2442 studio and my formal shop at Audu bako. We packed everything from shoes, bags, TVs, fridges, Ac's, Toys and other items from the former shops to this new shop as the shop owners asked us to leave their premises since we are no longer paying rent for another year. But everything was looted, they didn't even leave a pair of shoes. They packed all our AC and Flat screens, fridges and other valuables items. But we leave everything to God. And we can understand that some people have being looking for opportunity like this to loot some shops, they just use the excuse of #endsars and #endnorthbanditry protest to destroy properties and people's life. But we pray for a #newnigeria and we pray for peace in our country. Alhamdulillah for good health and peaceful life 🙏🙏🙏. #notowar #notoanarchy #staysafe #stayresponsible

A post shared by Mansurah Isah (@mansurah_isah) on



 Source: Legit.ng

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Wata sabuwa: Matasa sun fasa shagon Mansura Isah a Kano, sun kwashe komai "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?