--
 A Kano: An damke wani Malam Boka yana kokarin kwalkwalewa wani jariri ido don asiri

A Kano: An damke wani Malam Boka yana kokarin kwalkwalewa wani jariri ido don asiri


Wani Malam Boka a jihar Kano, Yahaya Shehu, ya shiga hannu bayan kokarin cire kwayan idon wani jariri, Ahmad, domin amfani da shi wajen aikin tsubbu. Wannan abu ya faru a unguwar Hotoro, karamar hukumar Nasarawa a jihar Kano, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito. 


Rahotanni sun nuna cewa Bokan ya yi wa wani Kabiru Sani alkawarin N8m da mota idan ya samo masa sabon jariri. Hukumar yan sandan jihar Kano ta tabbatar da aukuwan lamarin kuma ta ce tuni an damke Bokan. Kakakin hukumar, DSP Abdullahi Haruna kwaya, ya ce sun damkeshi ne bayan Kabiru Sani, ya kai kara ofishin yan sanda. 


"Bayan Sani ya je wajen Bokan domin neman magani, Bokan ya fada masa wani abu da zai gauraya da fitsarinsa kuma yayi wanka dashi na tsawon kwanaki uku," cewar Kakakin yan sanda Kiyawa. 


"Komawarsa bayan kwanaki uku, Bokan ya kara masa wani ruwa wanda hakan ya sa shi bin dukkan abinda ya umurcewa, har zuwa ranar da ya umurceshi ya dauka jaririn 'yar uwarsa domin a kwalkwale idonsa na hagu domin amfani." 


"Hakan ya sa ya je ya roki yar uwarsa ta kawo jaririnta domin amfani da shi wajen yiwa wani Soja aiki." "A lokacin ne 'yar uwar ta fahimci halin da ake ciki kuma ta kai Sani ofishin yan sanda inda aka bayyana musu abinda ake ciki," Ya kara da cewa ba tara da bata lokaci ba aka damke bokan a Hotoro. Ya ce an samu abubuwa irinsu makara, kasa, kwarya da wasu rubuce-rubuce a hannunsa. 


Source: Legit Newspaper 


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to " A Kano: An damke wani Malam Boka yana kokarin kwalkwalewa wani jariri ido don asiri "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?