--
Wata Sabuwa: Nan da makonni biyu daruruwan yan Najeriya zasu kamu da Korona - Gwamnatin tarayya

Wata Sabuwa: Nan da makonni biyu daruruwan yan Najeriya zasu kamu da Korona - Gwamnatin tarayya


Gwamnatin tarayya ta bayyana illar da zanga-zangan #ENDSARS za ta yiwa da yaki da COVID-19 - Kwamtin PTF ta yi zamanta kaman yadda ta saba a ranar Litinin 


Shugaban kwamitin ya na da tabbacin yaduwar cutar cikin yan zanga-zangan Kwamitin fadar shugaban kasa na yaki da cutar COVID-19, ta shiga jerin masu kira ga matasa masu zanga-zangar #ENDSARS su sassauta kuma su amince da sulhu saboda har yanzu akwai cutar Korona a gari. 


Sakataren gwamnatin tarayya kuma shugaban kwamitin, Boss Mustapha, ya bayyana hakan ne ranar Litinin a hira da manema labarai a Abuja, The Sun ta nakalto Mustafa ya siffanta masu zanga-zangan a matsayin manyan masu iya yada cutar kuma za'a fara ganin sakamakon hakan nan da makonni biyu masu zuwa. 


"Maganar gaskiya shine, nan da mako biyu masu zuwa, idan ka tattara dukkan masu taro a Lekki Toll Plaza, za ka samu masu cutar da dama, " Mustafa yace. "Duk inda mutane suka taru kuma basu bin sharrudan kariya daga cutar irinsu bada tazara, amfani da rigar rufe baki da hanci, tsafta da gudun taro, wajibi ne a yada cutar, ko ana so, ko ba'a so."


"Saboda haka ina da tabbacin cewa nan da makonni biyu, idan aka tattaro masu taro a Lekki Toll Gate da Unity Fountain dake Abuja da wuraren da ake zanga-zanga. Zamu yi fama da masu cuta da yawa nan da makonni biyu." 


Jiya mun kawo muku cewa hukumar da ke dakile yaduwar cututtuka ta Nigeria (NCDC), ta tabbatar da cewa sabbin mutane 118 sun kamu da cutar COVID-19 a ranar Litinin, 19 ga watan Oktoba 2020. Hukumar NCDC a shafinta na Twitter @NCDCgov, 


a daren ranar Litinin, ta wallafa cewa jimillar mutane 61558 ne suka kamu da cutar, yayin da mutane 56697 suka warke. Sai dai hukumar ta wallafa cewa, mutane 1125 ne Allah ya karbi rayuwarsu sakamakon yin jinya na wannan cuta. 


Source: Legit 


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Wata Sabuwa: Nan da makonni biyu daruruwan yan Najeriya zasu kamu da Korona - Gwamnatin tarayya "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?