--
Kungiya ta shirya taron ‘Yan Buhari na mutum Magoya miliyan 10 a Abuja gobe

Kungiya ta shirya taron ‘Yan Buhari na mutum Magoya miliyan 10 a Abuja gobe


I stand With Buhari za ta gudanar da wani babban tattaki a Ranar Laraba - Kungiyar ta I stand With Buhari ta ce ta na nan tare da gwamnatin Buhari 


A daidai wannan lokaci wasu na fama da zanga-zangar #EndSARS a kasar Wata kungiya mai suna ‘I stand With Buhari’, ta sanar da shugaban ‘yan sandan Najeriya a garin Abuja, shirinta na gudanar da tattaki na musamman.


Wannan kungiya za ta tara mutane miliyan goma da su fito domin nuna cikakkiyar goyon-bayansu ga tafiyar shugaban kasa Muhammadu Buhari. Shugaban wannan kungiya, Ogochukwu Ezeaku, ya shaidawa jaridar Punch wannan a lokacin da aka yi hira da shi a ranar 19 ga watan Oktoba, 2020. 


Mista Ogochukwu Ezeaku ya bayyana cewa su na sa ran za su samu goyon-bayan dakarun ‘yan sanda wajen shirya wannan tattaki a birnin tarayya. Ezeaku ya ce za su fara wannan tafiya ne daga Unity Fountain, a Maitama a ranar Larabar nan. 


Da aka tambaye shi ko za a samu sabani tsakaninsu da masu zanga-zangar #EndSARS, Ezeaku ya ce ya san masu fafatukar #EndSARS ba su tada rikici. Ya ce makasudin wannan tattaki shi ne a nuna wa Duniya cewa akwai dinbin mutanen da ke goyon bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari har gobe. 


Wannan kungiya ba ta kishiyantar masu zanga-zangar #EndSARS, kamar yadda ta bayyana. ‘I stand With Buhari’ ta ce za ta goyi bayan wancan tafiya ta kiran inganta sha’anin tsaro, muddin masu zanga-zangar ba su saki layi, sun koma takalar fada ba. 


A jiya ne jam’iyyar APC ta ce akwai lauje cikin nadi a tafiyar #EndSARS. Shugaban APC, Mai Mala Buni ya ce akwai makarkashiya a zanga-zangar da ake ta yi. Gwamnan na Jihar Yobe ya ce tsageru masu laifi ne ke jin tsoron Dakarun SARS da aka rusa. 


Source: Legit.ng


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Kungiya ta shirya taron ‘Yan Buhari na mutum Magoya miliyan 10 a Abuja gobe "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?