--
Na yi nadamar goyon bayan shugabanni marasa kishin kasa - Fatima Ganduje Ajimobi

Na yi nadamar goyon bayan shugabanni marasa kishin kasa - Fatima Ganduje Ajimobi


Fatima Ganduje -Ajimobi, diyar gwamnan jihar Kano, ta yi wallafa inda ta nuna damuwarta - Ta bayyana cewa, ta rasa me za ta ce amma tana matukar jin kunyar abinda tayi 


Ta yi nadamar taba goyon bayan shugabanni marasa hankali da kuma rashin kishin kasa Diyar Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, Fatima Ganduje Ajimobi, wacce ke auren dan marigayin tsohon sanata kuma gwamnan jihar Oyo, ta yi magana a kan shugabanni. 


Fatima Ganduje Ajimobi ta ce ta rasa me za ta ce a wallafar da tayi amma tana matukar nadama. 


Ta bayyana damuwarta tare da dana-saninta na goyon bayan shugabanni "marasa hankali kuma marasa kishin kasa." Kamar yadda ta wallafa, "Na rasa me zan ce kuma ina matukar jin kunya da na taba goyon bayan shugabanni marasa hankali da kuma kishin kasa." 



Fatima ta yi wannan wallafar ne bayan sa'o'i kadan da yin harbe-harbe ga masu zanga-zangar bukatar kawo karshen cin zarafin 'yan sanda ke yi a Lekki tollgate da ke jihar legas. 


A wani labari na daban, Sifeta janar na 'yan sandan Najeriya IGP Mohammed Adamu, ya bada umarnin janye dukkan 'yan sandan da ke tsaron lafiyar manyan mutane a fadin kasar nan. 


Kamar yadda aka gano, wannan hukuncin ya biyo bayan bukatar sake assasa dokar dakile zanga-zangar EndSARS a tituna. 


Wannan umarnin na kunshe ne a wani sako da aka mika ga dukkan kwamandojin 'yan sandan kasar nan a ranar Litinin wanda jaridar The Cable ta gani. 


A umarnin, wanda zai fara aiki a take, gidajen gwamnati, shugaban majalisar dattawa da kuma kakakin majalisar wakilai ne aka tsame. 



"Sifeta janar na 'yan sandan Najeriya ya bada umarnin janye dukkan 'yan sandan da ke tsaron manyan mutane banda na gidajen gwamnati, shugaban majalisar dattawa da kakakin majalisar wakilai," sakon yace. 


Source: Legit

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Na yi nadamar goyon bayan shugabanni marasa kishin kasa - Fatima Ganduje Ajimobi "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?