--
Kamuwa da Coronavirus: Buhari ya jajantawa Donald Trump kuma yayi masa addu'a

Kamuwa da Coronavirus: Buhari ya jajantawa Donald Trump kuma yayi masa addu'a


Buhari ya bi sahun shugabannin kasashen duniya wajen jajantawa Trump da matarsa - Trump ya killace kansa da iyalansa bayan kamuwa da cutar Korona 

Trump ya kamu ne bayan zuwa kamfe da daya daga cikin hadimansa Shugaba Muhammadu Buhari ya aika addu'o'insa ga shugaban kasan Amurka, Donal Trump, da uwargidarsa, Melania Trump, da suka kamu da cutar COVID-19. 


Buhari ya aike sakonsa a jawabin da ya saki ranar Juma'a a shafinsa na Tuwita. A cewarsa, kamuwa da cutar da Trump yayi ya nuna cewa irin hadarin da cutar ke da shi ga duniya gaba daya. "Ina yiwa shugaban kasan Amurka, Donald Trump, da uwargidarsa, Melania, samun lafiya daga cutar COVID-19." Yace 



Mun kawo muku rahoton cewa Shugaban kasar Amurka Donald Trump da matarsa Melania sun kamu da COVID 19 da aka fi sani da korona kimanin kwanaki 31 kafin zaben shugaban kasa na shekarar 2020 a kasar. 


Shugaban kasar ya tabbatar da hakan a shafinsa na Twitter bayan daya daga cikin hadimansa Hope Hicks ya kamu da cutar tunda farko. "A daren yau, ni da @FLOTUS mun kamu da COVID 19. Za mu killace kanmu ba tare da bata lokaci ba. Za mu ci gallaba a kan wannan tare!" kamar yadda ya rubuta. 


Source: Legit.ng


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: 

0 Response to "Kamuwa da Coronavirus: Buhari ya jajantawa Donald Trump kuma yayi masa addu'a "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?