--
Bai kamata a saurari ma su zanga-zangar ENDSARS ba - Bidiyon Jarumi Zaharaddeen Sani

Bai kamata a saurari ma su zanga-zangar ENDSARS ba - Bidiyon Jarumi Zaharaddeen Sani


Jarumi a masana'antar shirya fina-finan Hausa (Kannywood), Zaharaddeen Sani, ya bayyana ra'ayinsa a kan zanga-zangar ENDSARS 


Zangar-zangar neman a soke rundunr SARS ba ta samu karbuwa ba a jihohin arewa maso yamma da arewa maso gabas 


Wasu matasa a Maiduguri, babban birnin jihar Borno, sun gudanar da zanga-zangar nuna goyon bayan rundunar SARS Zaharadden Sani, Jarumi a masana'antar shirya fina-finan Hausa (Kannywood), ya ce a tunaninsa kuskure ne jama'a su ke gudanar da zanga-zanga a kan jami'an 'yan sanda ba 'yan bindiga da ke kashe mutane ba A cikin wani faifan bidiyo da Legit.ng Hausa ta ci karo da shi a dandalin sada zumunta, 


an jiyo Jarumin ya na bayyana cewa; "sai jami'an 'yan sanda za a yi wa zanga-zanga, me ya sa jama'a ba za su yi wa gwamnati zanga-zanga ba saboda 'yan ta'adda sai saboda dan SARS guda daya,? 


"Ko su 'yan bindiga tsoronsu ake ji? su na kashe mutane ba iyaka, amm ba za a iya fitowa a yi zanga-zanga saboda hakan ba, sai saboda laifin dan SARS guda daya.


"Ni a ganina hakan kuskure ne, bai kamata shugaban rundunar 'yan sanda ya sauraresu ba, ya fada mu su cewa aiki ya yi ma sa yawa, akwai aiyuka a gabansa da yawa, saboda 'yan bindiga su na ta kashe mutane," kamar yadda Jarumin ya bayyana. 




A ranar Litinin ne Legit.ng Hausa ta wallafa cewa a wani faifan bidiyo da jaridar The Cable ta wallafa an ga wasu ma su zanga-zanga sun hada kai tare da ceton wani dan sanda da wasu 'yan daba ke nufin cutarwa. 


Duk da babban sifeton rundunar 'yan sanda (IGP) ya sanar da cewa an rushe rundunar SARS, har yanzu fusatattun matasa ba su daina fitowa domin gudanar da zanga-zanga ba. 


A yayin da matasan ke cigaba da gudanar da zanga-zangar, wasu matasa a Maiduguri, babban birnin jihar Borno, sun gudanar da zanga-zangar nuna goyon bayan rundunar SARS a ranat Talata. Matasan sun bukaci a dawo da SARS sannan a tura jami'an rundunar zuwa jihar Borno domin su yaki 'yan Boko Haram. 


Source: Legit 


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Bai kamata a saurari ma su zanga-zangar ENDSARS ba - Bidiyon Jarumi Zaharaddeen Sani "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?