--
ArewaMufarka: Aisha Buhari ta kaddamar da wasu sabbin bidiyo a kan yakar rashin tsaro

ArewaMufarka: Aisha Buhari ta kaddamar da wasu sabbin bidiyo a kan yakar rashin tsaro

Uwargidan Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ta kaddamar da kamfen akan halin da kasa ta ke a ranar Asabar a shafinta na Twitter - Ta wallafa bidiyon wasu mutane 5 ne wadanda ke rike da takardu na neman taimakon gaggawa akan rashin tsaro dake Najeriya 


A cikin bidiyon, akwai waka mai taken aceci jama'a wadda hakan ya jawo cece-kuce a kafafen sada zumuntar zamani Uwargidan Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha Buhari, ta kaddamar da sabon kamfen akan rashin tsaron dake kasar nan a shafinta na Twitter. Kamar yadda ta kaddamar da kamfen din nata mai take 


"Mu farka Arewa", an nuno wasu bidiyoyi guda 2, wadanda ke nuna mutane 5 da takardu da aka rubuta "A kawo karshen rashin tsaro cikin gaggawa; A daina ta'addanci; rayuwarmu tana da muhimmanci ". Ta wallafa bidiyon ne da wata wakar Hausa, wadda har a shafinta na kafar sada zumuntar zamani ta Facebook, wadda hakan ya jawo cece-kuce kala-kala. 


Wadda wakar take nuna neman taimako na gaggawa wato Achechijamaa. Mutane fiye da 396,000 sun duba bidiyon Achechijamaa kuma sun yaba da kokarin uwargidan shugaban kasar. 




Source: Legit.ng

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "ArewaMufarka: Aisha Buhari ta kaddamar da wasu sabbin bidiyo a kan yakar rashin tsaro "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?