--
An kusa wajabtawa wa 'yan Najeriya mallakar lambar NIN - Isa Pantami

An kusa wajabtawa wa 'yan Najeriya mallakar lambar NIN - Isa Pantami


Nan ba da daɗewa ba za a wajabta wa dukkan yan Najeriya mallakar lambar shaiɗan zama ɗan kasa wato NIN 


Ministan Sadarwa da tattalin arziki na zamani, Dakta Isa Pantami ne ya bayyana hakan yayin da jam'ian NIMC suka ziyarce shi 


 Ministan ya ce mallakar lambar na da matuƙar muhimmanci ga duk wanda ke son amfana da ayyukan gwamnati da tallafi


Ministan Sadarwa ta tattalin arziki na zamani, Isa Pantami ya sanar da cewa nan gaba za a wajabta wa ƴan Najeriya mallakar lambar shaidar ɗan ƙasa NIN. Ministan ya yi wannan jawabin ne yayin da ya ke karbar baƙuncin tawagar hukumar samar da lambar ɗan ƙasa (NIMC) a ofishinsa da ke Abuja. 


Ya kuma bukaci hukumar ta ƙara adadin mutanen da ta ke yi wa rajista duk wata daga 500,000 zuwa miliyan 2.5. Har wa yau, Pantami ya umurci hukumar ta kafa cibiyoyin sauraron ƙorafin mutane a sassan kasar don warware matsalolin mutane. 


A cikin sanarwar da kakakin ministan Uwa Suleiman ta fitar an gano Pantami ya ce, "ya mayar da hankali don ganin ƴan Najeriya sun samu lambar shaiɗan zama yan kasa" kuma ya yi kira gare su suyi rajista ba tare da bata lokaci ba."


Ya ce; "Wannan na da muhimmanci don nan gaba mallakar lambar NIN zai zama wajibi don amfana da ayyukan gwamnati da tallafi. "Shaidar zama ɗan ƙasa ta zamani wajibi ga duk wata ƙasa mai son cigaba kuma ɗaya daga cikin ginshikin tsarin ɗoka."


Source: Legit 


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "An kusa wajabtawa wa 'yan Najeriya mallakar lambar NIN - Isa Pantami "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?