--
Za a yi juyin juya hali idan har Biden ya zama shugaban Amurka - Trump

Za a yi juyin juya hali idan har Biden ya zama shugaban Amurka - Trump

Trump ya bayyana musibar da za ta iya faruwa idan har Joe Biden ya zama shugaban kasar Amurka  Trump da magoya bayan jam'iyyar Republican sun caccaki Biden da jam'iyyarsa ta Democrat na gaza janye zanga zangar Antifa da Black Lives

Trump ya ce idan har Biden ya ci zabe to za a tayar da tarzoma da juyin juya hali a Amurka Dan takarar jam'iyyar Democrat a zaben Amurka Joe Biden mutum-mutumi ne, wanda idan aka zabe shi a Nuwamba, zai haifar da juyin juya hali a kasar,

cewar shugaba Donald Trump. "Biden ba zai iya kwantar da tarzoma ba," cewar Trump. "Za su karbe gwamnati. Su ne ke da nasara. Idan Biden ya ci zabe, su ke da nasara. Shi mutum ne mai rauni. "Don haka za a samu tashin hankali ...

Za su zo su kwace garuruwanku. Juyin juya hali ne. Kun fahimci haka. Wannan juyin juya hali ne kuma Amurukawa ba zasu laminta ba."

A cewar Trump, daukar nauyin juyin juya halin na zuwa ne daga "masu kudin da ke da mummunar manufa, amma ba zasu samu nasara ba, za su sha kasa."

A ranar Linitin, Biden ya zargi Trump da kasa dai daita al'ummar Amurka, hasalima yana raba kawunansu ne, kuma sakonnin shi suna wuce gona da iri da tayar da tarzoma. Martanin Biden yazo ne bayan da Trump da magoya bayan jam'iyyar Republican suka caccake shi da jam'iyyarsa ta Democrat na kaza janye zanga zangar Antifa da Black Lives.

Yan Republican sun ce Democrat a jihohin da suke da karfin iko suna kokarin yin kullalliya ne don tayar da tarzoma idan aka zo gudanar da babban zaben kasar. An gudanar da zanga zanga mai karfi kan nuna kin jinin wariyar launin fata a Amurka bayan da 'yan sanda suka kashe wani bakin fata George Flyod a ranar 25 ga watan Mayu.

A watan August, sabuwar zanga zanga ta fara a Wisconsin da wasu yankunan Amurka bayan da 'yan sanda suka harbe Jacob Blake, bakin fata dan kasar. Lamarin ya sanya kazamar arangama tsakanin 'yan sanda da fararen hula musamman ma bakaken fata 'yan Amurka, wadanda ke ganin ana nuna masu wariyar launin fata.


Source: Legit.ng

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Za a yi juyin juya hali idan har Biden ya zama shugaban Amurka - Trump "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?