--
‘Yadda na fara sana’ar kayan sawa na haya a Kano’

‘Yadda na fara sana’ar kayan sawa na haya a Kano’

Wani matashin tela da ya fara sana’ar bayar da hayar kayan sawa birnin Kano na kara samun karbuwa.

Ibrahim Yakubu ya ce akalla mutum 300 na tuntubarsa a kullum cikin mako guda da bude wurin bayar da hayar kaya da ya fara a ranar 24 ga watan Agusta, 2020.

“Na lura cewa akwai kashe kudui mutum ya sayi yadi ya dinka, shi ya sa ni nake sayen yadika nake dinkawa sannan in bayar da hayar kayan.

Karin farahin wutar lantarki ya tayar da kura
Mun sasanta a Muhammad Babangida —Rahma Indimi
Ibrahim mazaunin unguwar Tal’udu a garin Kano, ya samu kwarin gwiwar fara sana’ar ne da jarinsa na kimanan N30,000 da nufin samar wa mutanen kayan fita kunya a wuraren buki da sauran taruka.

“Muna bayar da hayar atamfar mata ko shadda ta maza a kan N1,500, Getzner kuma N3,000 sannan lokacin haya daga 9.00 na safe ne zuwa 10.00 na dare”, inji Ibrahim.

Matashin ya ce da farko mahaifansa sun dauke shi mashiririci da ya shaida musu abin da yake son yi, amma hakan bai sa ya karaya ba cewa abin da zai yi zai biya wa mutane bukata.

Ya yi kira ga matasa da su dage da neman na kansu ta hanyar kasuwanci, domin “jiran sai mahaifanka sun ba ka ba zai wadatar da kai ba”, inji shi.



Source: Aminiya Daily Trust

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "‘Yadda na fara sana’ar kayan sawa na haya a Kano’"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?