LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Babu ranar fita: An yankewa jarumin da yake yin fim din batsa hukuncin shekaru 250 a gidan yari

Wani jarumi da yake yin fim din batsa za a yanke masa hukuncin shekaru 250 a gidan yari,

An kama shi da laifin yiwa mata da yawa fyade ciki kuwa harda karamar yarinya Mutumin mai suna Ronald Jeremy Hyatt, dama can ya jima a gidan yari, inda aka bukaci ya biya belin $6.6m


An kama jarumin fim din batsa, Ron Jeremy, da laifuka guda ashirin da suke da hadi da cin zarafin mata 12 da kuma yarinya karama, da aka gano tun a shekarar 2004, cewar ofishin alkalin-alkalai na Los Angeles.

Mutumin wanda yake da shekaru 67, da ainahin sunansa yake Ronald Jeremy Hyatt, an kama shi da laifuka a watan Yuni da suka hada da fyade guda uku. Haka kuma ya amsa laifinsa.

A ranar Litinin ne 31 ga watan Agusta, aka sake gano wasu laifuka guda 20 da Jeremy ya aikata, inda aka bayyana cewa ya yiwa mata 13 fyade tun a shekarar 2004.

An kama Jeremy dai ya yiwa wata yarinya 'yar shekara 15 fyade a lokacin da take bacci, inda ya sanya mata wani abu a gabanta.

An ce Jeremy ya yiwa yarinyar fyade ne a shekarar 2004, haka kuma ana zargin shi da yiwa wata mata fyade a cikin wannan shekarar.

An bukaci Jeremy ya dawo kotu a cikin watan Oktoba. Idan aka same shi da duka laifukan da ake zargin shi dasu, za a yanke masa hukuncin shekaru 250 a gidan yari.


A yadda wani rahoto na yanar gizo ya bayyana, tuni dama Jeremy yana gidan yari a Los Angeles, inda ake tsare dashi tare da sanya belin dala miliyan shida da dubu dari shida ($6.6m).


Source: Legit.ng

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments