LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Wata sabuwa: Daga yanzu babu ruwanmu da farashin man fetur - FG

PPRA, hukumar gwamnatin tarayya da ke da alhakin kayyade farashin man fetur, ta ce daga yanzu babu ruwanta da maganar farashin mai, magana ta koma hannun 'yan kasuwa.

Jaridar Punch ta rawaito cewa babban sakataren hukumar PPRA, Abdulkadir Saidu, ne ya sanar da hakan. A cewar jaridar Punch, Saidu ya bayyana cewa daga yanzu kayyade farashin litar mai zai dogara ne a kan bukatarsa da kuma farashin danyen mai a kauwar duniya.

Hakan na nufin gwamnati ta tsame hannunta daga tsayarwa ko kayyade farashin litar mai. Saidu, wanda babban manaja a PPRA, Victor Shidok, ya wakilta, ya ce PPRA za ta cigaba da sa-ido a kan farashin da 'yan kasuwa ke sayar da litar mai domin tabbatar da cewa ba a zalunci jama'a ba.

"Alhakinmu ne mu tabbatar da cewa mun kare hakkin jama'ar da ke sayen man fetur domin amfaninsu," a cewar Saidu.

A cewar Saidu, har yanzu 'yan kasuwa basu fara shigo da tataccen man fetur ba saboda karancin kudaden kasar waje a kasuwar canjin kudade.

An gaza cimma matsaya a tsakanin 'yan kasuwa da hukumar NNPC a kan tsayar da farashin litar mai a gidajen mai mallakar 'yan kasuwa. Kungiyar dillalan man fetur ta sha bayyana cewa ba zata iya sayar da litar man fetur a kan farashin da gwamnati ta tsayar ba.

'Yan kasuwa na kafa hujja da cewa zasu yi asara matukar suka sayar a farashin gwamnati saboda suna kashe kudin dako. A makon jiya ne gwamnatin tarayya ta sanar da kara farashin litar man fetur, lamarin da ya harzuka 'yan najeriya da dama.

Kungiyar daliban Najeriya (NANS) ta fadawa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya janye karin farashin man fetur da gwamnatinsa ta yi ko kuma dalibai su mamaye titunan Najeriya a wata gagarumar zanga-zanga da bai taba ganin irinta ba.

NANS ta ce ta yi matukar girgiza da jin labarin cewa gwamnati ta sanar da yin karin kudin litar man fetur daga N145 zuwa N161. A cikin wani jawabi da mataimakin shugaban kungiyar, Kwamred Ojo Raymond, ya fitar, NANS ta bayyana karin farashin man fetur a matsayin almara, tunzura jama'a da kuma nuna zallar rashin tausayi.

Source: Legit.ng

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments