LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Tirƙashi: An kama wani mutum ya saci motar FRSC a Abuja


Yan Sanda da ke birnin tarayya Abuja sun kama wani mutum da ya saci mota mallakin hukumar kiyayye haɗɗura ta ƙasa, FRSC, daga hedkwatar hukumar da ke Wuse Zone 5, Abuja. Sanarwar da mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Abuja, DSP Anjuguri Manzah ya fitar ta ce an kama Hamisu Tukur mai shekaru 25 ne yayin bincike da hukumar ke yi a titi. 


"Bayan rahoton da rundunar ƴan sanda ta Abuja ta samu, rundunar a ranar 5 ga watan Satumban 2020 ta kama wani Hamisu Tukur mai shekaru 25 a kusa da Bwari saboda sace wata mota mallakar Hedkwatan hukumar kiyayye haɗɗura ta ƙasa FRSC da ke Sky Memorial, Wuse Zone 5. 


"Yan sandan yankin Bwari ne suka cafke wanda ake zargin yayin bincike da suke yi bayan rahoton da hukumar ta FRSC ta shigar wa ƴan sanda. "An kama wanda ake zargin da mota ƙirar Toyota Hilux HQ-26RS mai launin fari da makulli ƙwara ɗaya. 


"Hukumar yan sandan ta tabbatar wa al'umma cewa za ta cigaba da gudanar da aikin ta na kiyayye rayyuka da dukiyoyin su kuma ta yi kira garesu su rika kiran wadannan lambobin don shigar da rahoto: 08032003913, 08061581938, 07057337653 da 08028940883. "Za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu idan an kammala bincike a kansa," a cewar sanarwar. 


A wani labari na daban, hukumar yan sandan Najeriya ta bayyana cewa za ta tura akalla jami'ai 30,000 jihar Ondo domin tabbatar da tsaro a zaben gwamnan jihar da zai gudana ranar 10 ga Oktoba. Vanguard ta ruwaito cewa kwamishanan yan sandan jihar, Bolaji Salami, wanda ya bayyana hakan a Akure, 


birnin jihar, ya ce ba za'a hana yan kasashen waje shiga jihar lokacin zaben ba. "Hedkwatar hukumar yan sanda ta tura jami'ai 30,000 dukkan kananan hukumomi 18 dake jihar. "Insfekta Janar na yan sanda ya bada umurnin cewa a tura yan sanda hudu kowani rumfar zabe 

domin bayar da tsaro. An yi hakan ne domin tabbatar da zaman lafiya da tsaron masu zabe a jihar. "Hakazalika an shirya samun taimako daga sauran hukumomin tsaro." A cewarsa. 


Source: Legit.ng

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments